“Macen da ta tsorata da takobi, ba ta cancanci mallakar gida ba – Queen Amina
Daga AISHA ASAS
Mace wata halitta ce da idan na ce kaf a duniya ba a taɓa halittar wani abu mai tarin baiwa, mai hikima da kuma hangen nesa ba irinta ban yi kuskure ba.
Mace kamar yadda masana suka tabbatar na ɗauke da wata baiwa ta musamman da ba kasafai ka ke iya samun ta a wasu halittu ba, ita ce baiwar yin ababe fiye da ɗaya a lokaci guda.
Sau da yawa za ka samu namiji jarumi da ke da baiwa mai tarin yawa, wanda duniya ke kallo a matsayin jagora, amma sai ka same shi yana kallon yadda mace ke iya ababe da dama a lokaci guda a matsayin babban lamari, dalilin shi ɗin ba zai iya yin hakan ba.
Wannan ne ya sa a duk wata hanya da mace ta bi, ko wani aiki da ta ɗauka wanda duniya ke ganin kamar an ƙirƙire shi ne domin maza, za ka samu ƙwarewa a tare da ita tamkar don ta aka yi.
Hakan na da nasaba da irin ƙwarewar da aka bata kan kowane ɓangare ta kurɗa. Saidai bayan duk wannan sai a ka saka mata rauni, wanda ya rufe wannan baiwar, hakan ne ya sa idan ana kallon wannan raunin ne ake mamakin yadda suka iya ɗaukar abinda aka ajiye don maza.
Sarauniya Amina ta Zazzau ɗaya ce daga cikin misalan da za mu iya kafa hujja da su a wannan ɗan bayanin da muka yi.
Ga waɗanda ba su san ko wa ake cewa ƙueen Amina ba, shafin Gimbiya na wannan mako zai samar maku da wannan ilimin, a kyauta. Idan kun shirya, zan ce a sha karatu lafiya.
Shin wacce ce Sarauniya Amina ta Zazzau?
A cikin tarihin ƙasar Hausa, babu wata mace da ta yi fice kamar Sarauniya Amina ta Zazzau. Sunanta ya yi amon da ya karaɗe Afirka da ma maƙwabtan ta, yayin da suke kiran sunanta da alfahari.
Idan mun kalli irin tasirin ta a ƙasar Hausa, za mu fahimci cewa, tabbas ba ƙaramar rawa ta taka ba duba da yadda bahaushe ya ɗauki darajar mace. Hakan na nufin ta kasance mace mai ƙarfin hali, jajircewa da ta tabbatar da cewa, mace ma na iya zama jagora, jaruma da za ta iya yin yaƙi, ta kuma yi nasarar kafa daula.
A yau, idan aka ambanci sunan Sarauniya Amina, tunani kan tafi kan irin ƙarfi da ƙoƙarin da ta yi wa ƙasarta, wannan ya sa har yanzu ake cewa: ” Amina ta Zazzau jarumar mace mai mulkin da ya kai ga masarautu da dama.”
Amina ya fito ne daga gidan sarauta ta birnin Zazzau wadda a yanzu ake kira da Zaria. An haife ta kimanin ƙarni na goma sha shida (c. 1533 CE). Mahaifinta shi ne sarkin Zazzau Nikatau. Mahaifiyarta kuwa ita ce Sarauniya Bakwa Turunku, wacce ita ma ta yi mulki bayan mutuwar mijinta.
Da wannan za mu iya cewa gadon ya kasance ta ɓangarori biyu a wirin sarauniya Amina, wanda hakan ya sanya tun tasowarta ta kasance mai ilimi kuma take samun kulawa wanda da dace daidai da gidan sarauta.
Tun a ƙurciyarta, Sarauniya Amina ta taso da son sanin ababe da yawa, don haka ta yi fice fiye da sauran ‘yan uwanta a ɓangaren ilimi. An haikanto jarumtarta tun a lokacin da take ƙarama, domin a lokacin da tsaranta ke zuwa wasa a dandali ko wasan ƙasa, Amina ta mayar da hankali kan koyon yadda ake ɗaukar takobi da kuma hawa doki. Waɗannan ne ƙimshiƙai biyu da kowane jarumi ke mayar da hankali kansu.
Masana tarihi sun bayyana ta a matsayin kyakyawar mace, saidai jarumtarta da son mullki ya luluɓe wannan kyawon nata, inda mutane ke fara hango su kafin kyan nata.
Wannan na daga dalilan da ya sana tun a ƙananan shekarunta ta kasance cikin ayarin ‘mayaƙan gida’ wato jaruman cikin gidan masarauta.
Ta koyi dabarun faɗa, dabarun jagoranci da kuma kasuwanci, kasancewar a lokacin Zazzau cibiya ce ta kasuwanci wadda ke ɗaukar ‘yan kasuwa daga wurare da dama, kamar Kano, Katsina da Borno.
Ba a ɗauki tsawon lokaci ba, Amina ta yi fice wurin jagorantar ƙaramar rundunar mata mayaƙa don bayar da horo. An ruwaito cewa, duk lokacin da aka shirya motsa jiki, ko wasannin mayaƙa, ita ce ke jagoranta, kasancewar irin ƙwazo da kuzarin da take nunawa wanda ya kere na ‘yan uwanta maza. Wannan ne ya sa ake kiranta da laƙabin ‘yar uwar jarumai.”
Idan za mu ci gaba da bayyana irin ƙwazo da bajintar da Sarauniya Amina ta nuna yayin ƙurciya, tabbas za mu iya ƙarasa adadin kalmomin wannan shafi ba tare da mun kammala ba, don haka bari mu tsakaita don zuwa ga lokutan da ta karɓi mulki wanda a nan ne tarihin ta da duniya ke faɗa ya samo asali.
Bayan rasuwar mahaifin Sarauniya Amina, mahaifiyarta Bakwa Turuku ce ta gaje shi. Kuma da Allah ya yi mata cikawa, sai aka naɗa ɗan uwan Amina mai suna Karama a matsayin sabon sarki.
Da sarki Karama ya rasu ne, manyan ‘yan majalisar masarauta da wasu sarakunan suka taru, suka yi matsaya ta ɗora Amina a kan kujerar mulki. Ba kuwa don komai suka yi haka ba face duba da irin ƙwarewarta da kuma jarumtarta waɗanda suka kasance manyan makamai na nasarar kowacce masarauta.
Wannan ya faru ne a tsakanin shekara ta 1576 CE, inda ta zama Sarauniya Amina ta Zazzau, mace ta farko a tarihin ƙasar Hausa da ta hau gadon sarauta da cikakken iko, saɓanin baya da mata ke hawa ta sanadin rashi ko kuma riƙo ba.
Abu na farko da Sarauniya Amina ta fahimta game da mulki, wanda shi ya sa ta zama sarauniya ta musamman shi ne, ta fahimci cewa, mulki ba kawai zama a fadar sarauta kana yanke hukunci ba ne. Ta faminci mulki a matsayin kare ƙasa daga abokanen gaba, bunƙasa tattalin arziki da kuma shimfiɗa tsari da zai ɗore ta fuskar dokoki da kuma walwalar al’umma.
Da wannan ne ta kafa tsarin mulkinta inda take jagorantar yaƙi don kare ƙasarta da kuma kafa tsarin kasuwanci a lokaci guda.
Sarauniya Amina ta Zazzau ta kasance jarumar da ke jagorantar rundunanta a yaƙi, wanda kusan duk yaƙin da ƙasarta ta yi kaso mai nauyi cikinsu ita ce a gaba. Masana tarihi sun tabbatar da ta yi yaƙe-yaƙe da ƙasashe da dama kamar; Katsina, Kano, Nupe, Kwararafa, Borno da sauransu.
Duka waɗannan yaƙe-yaƙen sun samu nasarar faɗaɗa ikon Zazzau, ta yadda ta samu nasarar mayar da daular babbar cibiyar ciniki dakuma siyasa a Arewa.
Masana sun ce, a duk wani yaƙi da Sarauniya Amina ta yi, kuma ta samu nasara, tana gina katanga a garin da ta ci yaƙin don tsaro, wanda su ne har yanzu muka sani da “Ganuwar Amina” wasu daga cikinsu suna nan a sassan Zaria, Kano, da Bauchi.
Haka ma a ɓangaren kasuwanci, Sarauniya Amina ta yi tsayin daka wurin gina tattalin arzikin ta hanyar tsara hanyoyin kasuwanci tsakanin Zazzau da sauran dauloli. Ta ƙarfafa ciniki da maƙwabta, musamman a kasuwannin ƙasar Nupe da Borno, inda ake siyar da gishiri, kayan ado da auduga.
Ta kuma gina tsarin haraji wanda ya taimaka wurin kula da sojojinta da gina katangu. A cikin fadar Zazzau kuwa, ta tanadi wurin ajiyar dukiya, kuma ta yi tanadin doka kan adalci da kare marasa ƙarfi.
Idan mun juya kan ɓangaren yadda raywar Sarauniya Amina ya amfani mata, inda shafin namu ya fi karkata, Sarauniya Amina ta kasance mai ba wa mata ƙwarin gwiwa tare da tabbatar masu za su iya yin komai matuƙar sun sa kansu.
“Mace idan ta tsorata da taboki, ba ta cancanci mallakar gida ba,” inji Sarauniya Amina.
Wannan maganar na nufin mata na da ikon tsayawa da ƙafafunsu wajen kare kansu, iyalansu da ƙasarsu. Hakan na nufin ƙimar mace a idonta ta sa take ganin tunda dai za ta iya, kowacce mace ma za ta ita matuƙar ta sa kanta.
Har ila yau, ta buɗe ƙofar shiga jerin jagororin dakarun yaƙi ga wasu mata, wanda hakan ya kasance sabon abu, kasancewar a baya ba hakan ba ne. Ta ƙarfafa cewa, mace ma za ta iya zama jagorar soji ko jagora a cikin kasuwanci ko siyasa matuƙar an bata dama.
Sarauniya Amina ta kasance gwana a maganganun hikima, inda sau dayawa ake amfani da kalamanta don ilimantar da wasu.
Bari mu yi duba wasu daga cikin ire-iren waɗannan maganganu;
Ta tafa faɗa cewa, “Mulki ba a fuska yake ba, a zuciya yake.” Ma’ana ƙarfi da ikon mulki ba wai
jinsi ne ke bayar da shi ba, yana samuwa ne ta zuciya da basira.
Ta kuma taɓa maganar da ta kasance zaburarwa ga mata, inda take cewa, “Ina son mace ta fi kowa tsoron Allah, ba tsoron duniya ba.” Wannan wani kira ne ta yi ga mata cikin hikima, wanda ke nuni da cewa, addini da kamun kai ne ginshiƙin kowacce mace tagari.
Kalaman ta ba su tsaya a iya mata ba, domin takan yi wasu zuwa ga rundunar yaƙinta, inda aka ruwaito ta taɓa faɗar cewa, “Ba wanda zai gina ganuwa idan zuciyarsa ta rushe.” Wannan na nufin mutum ya fara gina ƙarfin zuciyarshi kafin ya yi yunƙurin gina duniya. Hakan na nufin wanda ba jarumi ba ba zai iya taimakon ƙasarsa ba.
Kamar yadda aka sani, rayuwa zuma ce da maɗaci, wadda a wasu lokutan zaƙin kan rinjaye ɗacin, a wasu kuwa ɗanɗanon ɗacin ne zai mamaye bakinsu har su fara tsammanin ba za su taɓa jiyo zaƙin da ake faɗa ba.
Saidai a duk yadda rayuwa ta zo wa bawa, zai amince cewa, babu wata nasara da ba ta tare da ƙalubale. kamar yadda kuka sani ba wanda za a ambaci sunansa a matsayin gwani da a cikin rubutun rayuwarsa ba ka tarar da ƙalubale ba.
Ita ma Sarauniyar Zazzau ba ta fita daban ba, domin duk da ta yi fice, kuma ta zama jaruma da ake jin tsoron ta, hakan bai hanata fuskantar matsaloli a tafiyar ta ba.
ƙalubale na farko da ta fara cin karo da shi shi ne yadda wasu maza masu faɗa a ji a masarautarta suka ƙi amincewa da mace ta samu irin ƙarfin da ta samu, don haka suka yi amfani da masu ra’ayi irin nasu a cikin birnin don ganin sun rage mata tasirin da take da shi ta zama mace sarauniya mai cikakkiyar iko.
Haka kuma ta samu ƙalubale ta fuskar abokan gaba waɗanda suka yi ƙoƙarin amfani da birnin na Zazzau don kai mata hari ta hanyar ƙoƙarin ganin sun rusa haɗin kai da ke cikin birnin wanda ya kasance ginshiƙi na zaman lafiya.
A gafarce mu, za mu dasa aya anan, kuma da yardar mai duka, za mu kawo ƙarshen wannan tarihi na rayuwar jarumar ƙasar Hausa, ƙueen Amina of Zazzau a mako mai zuwa.
