Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD
Daga rikicin Wike a Abuja zuwa Fashola da sojoji a Legas – yadda zafafan muhawarori suka taso tsakanin farar hula da rundunar soja tun bayan komawar mulkin farar hula a 1999.
Tun bayan da sojoji suka miƙa ragamar mulki ga farar hula a shekara ta 1999, an sha samun taƙaddama mai zafi tsakanin wasu manyan ’yan siyasa da jami’an soja a wurare daban-daban na ƙasar. Duk da cewa rundunar sojin Nijeriya ta yi alƙawarin biyayya ga shugaban ƙasa da tsarin mulkin ƙasa, wasu lokuta sun nuna rikice-rikicen rashin fahimta da rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.
Ga yadda wasu daga cikin irin waɗannan al’amura suka faru da suka fi ɗaukar hankalin jama’a:
1. Nyesom Wike – Ministan Abuja:
A ranar 11 ga Nuwamba, 2025, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya samu saɓani da wasu jami’an rundunar ruwa yayin duba wani fili a yankin Gaduwa. Sojojin sun hana tawagarsa shiga wurin, lamarin da ya haifar da zafafan muhawara.
Wike, cikin fushi, ya soki matakin da sojojin suka ɗauka yana mai cewa “ba wanda ya fi doka girma,” yana zargin cewa an yi amfani da ƙarfin soja don take hakkin gwamnati.
“Ba zan bari wani ya raina gwamnati ba. Ba wanda ke sama da doka,” inji shi cikin ɓacin rai.
Daga bisani, ya bayyana cewa ofishin FCTA ba shi da wani takardar da ke tabbatar da sahihancin mallakar filin, yana mai alƙawarin shawo kan lamarin cikin gaskiya da doka.
2. Babajide Sanwo-Olu – Gwamnan Jihar Legas:
A shekarar 2023, Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya tsunduma cikin taƙaddama da wani soja bayan ya kama shi yana tuƙa babur a kan hanya da aka haramta (one way).
Gwamnan, wanda ke cikin jerin gwanon motoci, ya bi sojan har cikin bariki a Bonny Camp kafin ya sa a kama shi da kwace babur ɗinsa.
Wannan al’amari ya faru ne duk da cewa sojoji na cikin waɗanda aka keɓe daga haramcin “nawa babur” a wasu yankuna, amma Sanwo-Olu ya nace cewa “dokar doka ce, kuma babu wanda ya fi ƙarfinta.”
3. Babatunde Fashola – Tsohon Gwamnan Legas:
A ranar 16 ga Yuli, 2022, tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola, ya dakatar da wasu jami’an soja biyu da suka bi layin motar gwamnati (BRT lane) — layin da aka keɓe domin motocin sufuri na gwamnati.
Fashola ya nuna takaici cewa “waɗanda ya kamata su kare doka sune suke karya ta,” yana mai cewa rundunar sojin Nujeriya ta riga ta bayyana goyon bayanta ga tsarin dimokuraɗiyya, don haka ba za a lamunci irin wannan halayya ba.
Ya ƙara da cewa, “A Legas muna da siyasar bin doka — babu sassauci ga masu karya ƙa’ida, kowa ya tsaya cikin layi.”
4. Onyekachukwu Ibezim – Mataimakin Gwamnan Anambra:
Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra, Dr. Onyekachukwu Ibezim, shi ma ya sha rikici da sojoji a lokuta biyu — a 2022 da kuma a watan Nuwamba 2025.
A karo na farko, ya tsawata wa jami’an tsaro da ke kafa shingayen hanya a cikin Awka da Enugu, yana mai cewa hakan na haifar da cunkoso da wahala ga jama’a.
A karo na biyu, yayin zaɓen 2025, wani bidiyo ya nuna shi yana muhawara da jami’an soja a rumfar zaɓe a Awka.
Sai dai dakarun sojin sun fitar da sanarwa daga baya suna bayyana cewa an turo su ne bayan samun kiran gaggawa daga jami’an INEC da NYSC da aka rufe a hannun wasu ’yan daban siyasa.
Sun ce an “ɓata fassarar gaskiya” a yadda aka yaɗa lamarin, domin aikin su shi ne ceton ma’aikatan zaɓe, ba tsoma baki cikin siyasa ba.
Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Nujeriya, irin waɗannan muhawarori suna janyo tattaunawa game da iyakokin ikon farar hula da na sojoji. Yayin da ake ci gaba da jan layin bambanci tsakanin doka da iko, masana na cewa irin waɗannan lokuta na ƙara jaddada buƙatar a girmama tsarin mulki da bin dokokin ƙasa — ga farar hula da sojoji baki ɗaya.
