ISWAP ta kashe Janar Uba a Borno

Spread the love

A cikin wata sanarwa da ta rubuta da harshen Larabci, wacce ta wallafa a mujallar farfajiyarta mai suna Amaq, ƙungiyar ISWAP ta bayyana cewa ta kama Janar Uba kuma ta kashe shi bayan ta gudanar da bincike a kansa.

Shugaban Rundunar sojojin, M. Uba, wanda tun da farko rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya bayan mayakan ISWAP sun yi wa tawagarsa kwanton-bauna a hanyar Damboa zuwa Biu a Jihar Borno, yanzu an tabbatar da mutuwarsa.

Ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ta sanar da cewa ta kama Janar Uba kuma ta kashe shi, tare da sakin hotunan da ke nuna wannan mummunan aika-aika

Jaridar PRNigeria, wacce ke da kusanci da hukumomin tsaro, ta tabbatar cewa an sace Janar din kuma an kashe shi, duk da cewa rundunar soji ta yi tunanin ya tsira bayan harin farko.

A ranar Lahadi, ATP NEWS ta ruwaito – bisa ga wani rahoton HumAngle da ta samu, cewa an sace Janar Uba bayan ‘yan ta’addan ISWAP sun kai wa tawagarsa hari tare da jami’an CJTF a daren Juma’a.

Sai dai rundunar sojin ta musanta cewa an sace shi, tana mai cewa yana cikin lafiya ne bayan dakarunta sun fatattaki ‘yan ta’addan.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin, Laftanar Kwalal Appolonia Anele, ta fitar, ta tabbatar da cewa an yi wa dakarun 25 Task Force Brigade kwanton bauna, wacce Janar Uba ke jagoranta.

By Babaji