Yadda ƴata ta tsira bayan ƴan bindiga sun halaka mijina – Matar mataimakin shugaban makarantar Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matar mataimakin shugaban makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School, Maga na Jihar Kebbi da aka kashe, ta bayyana yadda ƴarta ta tsira yayin harin ƴan bindiga da ya yi sanadin awon-gaba da ɗalibai 25.

Rahotanni sun bayyana cewa, matar, mai suna Amina Hassan ta ce maharan sun kutsa gidansu ne da misalin ƙarfe 3:30 na asuba a lokacin da ƴan gidan suke barci.

Ta ce, da fari sun yi zaton hayaniya ce ta wasu dabbobi ne, inda ta faɗa wa marigayi mijin nata cewa sun fara lalata kayayyakin gida. A lokacin da ya tashi domin zuwa gani da ido, sai ya tarar da maharan riƙe da wasu muggan makamai.

“Mun fara jayayya da su. Sai ɗaya daga cikinsu ya ciro bindigarsa ya harbe mijina. Sannan sai suka janyo ni zuwa wajen gidan”, inji ta.

Daga nan sai ta nemi su rabu da ita inda ta ce, “Ba zan bi su ba tunda sun kashe uban ƴaƴana kuma suna faɗa wa yaran su koma ciki su yi barci.”

Ta bayyana cewa, ana tsaka da haka ne sai ƴarta ta fito, lamarin da ya sa suka rabu da ita sannan suka tafi da ƴar zuwa wajen kwanan ɗalibai.

“Daga nan ne sai suka ce mata ta kwanta domin su harbe ta ita ma. Sai ta ce musu, ‘na kwanta domin ku harbe ni?’ Sai suka ce eh.”

Ana tsaka da haka ne sai sai ta nemi su bata dama ta je ta zaga, inda suna buɗe ƙofar ɗakin kwanan ɗaliban sai suka ga sauran ƴan matan, lamarin da ya sa hankalinsu ya karkata daga ɓangaren yarinyar.

Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta bakin Kakakinta CSP Nafi’u Abubakar ta tabbatar da garkuwa da ɗaliban da halaka mataimakin shugaban makarantar, tana mai cewa tuni aka baza jami’ai a dazukan yankin da abin ya faru domin ceto ɗaliban.

By Babaji