Ku gaggauta ceto ƴan matan Kebbi – Tinubu ga hukumomin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta ceto ɗalibai mata guda 25 da aka yi awon-gaba da su a makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School, Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu na Jihar Kebbi.

Da fari, rundunar ƴan sandan jihar ta hannun kakakinta CSP Nafi’u Abubakar Kwatarkwashi, ta bayyana yadda aka yi garkuwa da ɗaliban a safiyar ranar Litinin.

A yayin haka ne aka halaka mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, da raunata mai gadinsu, Ali Shehu da harbin bindiga a hannunsa na dama.

Da yake sanar da umarnin Fadar Shugaban Ƙasa, Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris a wata takarda ranar Litinin, ya ce Shugaba Tinubu ya yi alla-wadai da harin, sannan ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da ba dukkan ƴan Nijeriya kariya musamman ɗaliban makaranta.

Akan haka ne kuma shugaban ƙasar ya umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su gaggauta nemo inda ɗaliban suke tare da ceto su, yana mai alwashin hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a ciki.

Ya kuma ce, gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an ceto ɗaliban duba da yadda gwamnatinsa ke cigaba da ƙoƙarin lamuran tsaro a ƙasar.

Kazalika, ya ce Nijeriya tana aiki tuƙuru wajen haɗa hannu da hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin ƙasashen Afirka da na ECOWAS da MNJTF domin daƙile ayyukan ta’addanci.

By Babaji