Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamna Muhammad kaula ya fitar ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya nuna alhininsa kan mummunan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a makarantar sakandaren ƙwararru ta ’yan mata a Maga, da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi.
Gwamnan ya la’anci harin da aka kai da dare wanda ya yi sanadin rasuwar mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, inda ya bayyana shi a matsayin mafi munin laifi.
Malam Dikko Raɗɗa ya jajanta wa Gwamna Nasir Idris da al’ummar Jihar Kebbi da iyalan waɗanda abin ya shafa kan wannan abin takaici.
Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen ceto ɗaliban da aka sace tare da kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki domin gurfanar da su a gaban shari’a.
“Wannan hari da aka kai wa makaranta ba kawai hari ne ga ilimi ba, har ma hari ne kan makomar mu gaba ɗaya,”Inji Dikko Raɗɗa.
“Ya zama dole mu kasance tsintsiya maɗauri ɗaya wajen yaƙar waɗannan miyagun mutane da ke barazana ga rayuwar ‘ya’yanmu,” in ji shi.
Gwamnan ya yi addu’ar samun kuɓutar ɗaliban da aka sace lafiya, tare da fatan dawowar zaman lafiya a faɗin ƙasar baki ɗaya.
