Mata A Yau

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (3)

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (3)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun kawo yadda za ki iya kula da fatarki, da kuma dabi'un da ya kamata mu dinga yi a lokacin sanyi. A yau za mu tabo wani bangare da ke bukatar kulawa a lokacin sanyi, wato kafa da kuma gashi. A lokacin sanyi ba iya fata ke shiga yanayi ba, asali ma ga wasu kafa ta fi shiga mawuyacin hali fiye da sauran fatar jiki. Kafa wata muhimmiyar vangare ce a jikin mutum da ya kamata a ba ta kulawa ta musamman a lokacin sanyi. Ta yaya za a iya kula da…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Aisha Asas barkanki da yau. Ya jama'a dai. To madalla. Don Allah ki taimaka min yadda ki ka saba ba wa mutane shawara da suke amfana da ita har ta yi masu aiki ga abinda yake ta damun rayuwarsu. Kina ji na ko, wato miji ne nake tare da shi da ban san kowanne irin mutum ne ba, ya sani duk daren Allah sai ya………..(mun cire kalmomin saboda rashin dacewar ta). Kuma kar ki ce sau daya, har ba iyaka. To wai yanzu na yi ciki, asibiti an ce Ina dauke da juna biyu na wata…
Read More
Ba abin da ya fi a rayuwar mace kamar ɗora ta kan hanyar ilimi – Mariya Durumin Iya

Ba abin da ya fi a rayuwar mace kamar ɗora ta kan hanyar ilimi – Mariya Durumin Iya

"Mace na rayuwa ne ƙarƙashin kulawar wasu har ƙarshen rayuwarta" Ci gaba daga makon jiya Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun fara shimfida kan tattaunawar da muke yi da daya daga cikin matan Arewa da suke da gidauniyar taimakon al'umma, inda muka soma da jin tarihin rayuwarta, yadda ta fara tunanin bude wannan gidauniyar da kuma hanyoyin da ta bi har hakarta ta cimma ruwa. A wannan sati, za mu soma ne da samar wa masu karatu amsar tambayar da muka kwana kanta, kamar yadda muka yi alkawari, kafi wasu tambayoyin su biyo baya. Har wa yau…
Read More
Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (2)

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (2)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun kwararo bayani kan yadda lokacin sanyi ke tasiri ga lalacewar fata da kuma gashin kai, sannan mun fara kawo wasu hanyoyin da za a bi don kaucewa lalacewar fata a lokacin. A wannan satin ma za mu ci gaba da darasin namu ne da karin wasu hanyoyi na kaucewa matsalar fata a lokacin hunturu. Yawaita shan ruwa: a lokacin sanyi, bukatuwar mu da ruwa kan ragu sosai ta yadda za ka iya daukar tsayin lokaci ba tare da ka ji bukatar ruwa ba, don haka muke kauce wa shan su, sai…
Read More
Duk wanda ya zama abin sha’awa a duniya mace ce ta mayar da shi hakan – Mariya Durumin Iya

Duk wanda ya zama abin sha’awa a duniya mace ce ta mayar da shi hakan – Mariya Durumin Iya

"Rayuwar maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya" Daga AISHA ASAS Rayuwar aure rai ne da ita tamkar dai yadda aka san dan adam da ruhinsa, yayin da mai shar'antawa Ya yi kira, ruhinsa ba zai kara ko sa'a daya a jikin ba, zai fice yana mai amsa kiran mahallici. Idan kuwa ba shi ya yi kiran nasa ba, ko duniya za ta taru don ganin ta tsayar da numfashinsa ba za ta iya tsayar da shi ba. Haka ita ma rabuwar aure, daga auren har ranar karewar sa rubatacce ne, idan ranar rabuwa ta zo,…
Read More
Ta yaya za ki kula da fatarki a lokacin sanyi

Ta yaya za ki kula da fatarki a lokacin sanyi

Daga AISHA ASAS Yayin da aka ce sanyi ya karato, mutane da yawa suna tausayawa halin da fatarsu za ta shiga yayin da suka yi arangama da yanayin na sanyi. A lokacin sanyi fata na yamushewa saboda yanayin iskar hunturu, kuma yakan yi muni musamman ga wadanda ba su san yadda za su ba wa fatar tallafi ba. Yanayin sanyi ba iya fata ya tsaya ba, domin hunturu na tava lafiyar gashi, ta hanyar yawan karyewa, sai kuma uwa uba kaushi ko fasau da kafa ke yi. Wadannan matsalolin na lokacin sanyi na sauya fasalin jiki tare da sanya shi…
Read More
Ilimin manya makami ne na gyara al’umma – Amina Ahmed Gumel

Ilimin manya makami ne na gyara al’umma – Amina Ahmed Gumel

"Rashin Turanci ne ke taka wa mutanen mu birki a Turai" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Amina Ahmed Sani Gumel 'yar Nijeriya ce wanda ta ke zaune a Kasar England inda ta ke koyar da ilimin manya masu koyon yaren Turanci a matsayin yare na biyu. A cikin tattaunawarta da wakilin manhaja, ta kawo irin hanyoyin da suke bi wajen koyar da mutane baqi yaren Turanci wanda zama ya kama su a Kasar England. Haka kuma ta kawo irin qalubalen da ta fuskanta wajen yaren Turanci dama irin nasarorin da ta samu a matsayin mai koyar da yaren Turanci a Kasar…
Read More
Yadda za ku gamsar da iyalinku yayin mu’amala ta aure (2)

Yadda za ku gamsar da iyalinku yayin mu’amala ta aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa mai zuwa kowanne mako a jaridarku ta Manhaja Blueprint. A makon da ya gabata mun kawo muku wasu bayanai a kan yadda ma'aurata za zu samu damar daɗewa a yayin da suke tarayyar aure. Ba shakka waɗannan dabaru da ƙanina ya rubuto za su taimaka matuƙa wajen samun gamsuwa tsakanin ma'aurata. A makon da ya gabata mun fara kwararomuku bayanai, sai muka tsaya saboda sarari ya cika. Yanzu sai ku gyara tabaronku don cigaba da karanta bayanai daga makon da ya gabata.…
Read More
Dandalin shawara: Ƙawa nake so kyakyawa kuma mai kuɗi

Dandalin shawara: Ƙawa nake so kyakyawa kuma mai kuɗi

Daga AISHA ASAS Salam. Asas ina wuni. Ya aiki. Ki daure ki amsa tambaya ta don Allah. Tun kwanaki na yi ta turo wa kina share ni. Don darajar iyayenki ki duba lamari na. Na kasance tun Ina ƙarama ban yi sa'ar ƙawaye ba, don ba su so na saboda Allah. Da na girma suka yi ta min ababe da dama na cutarwa. Har na haƙura a farko, sai dai na ce bari na nemi ki shawara, don Allah yadda zan samu ƙawa ta gari, mai kyau kuma wadda gidansu masu kuɗi ne, don kada ta so ni don abinda…
Read More
Dandalin shawara: Ina neman dabarun da saurayina zai dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Dandalin shawara: Ina neman dabarun da saurayina zai dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Assalamu alaikum. Aunty Aysha, ya ki ke? Ya yara? Don Allah shawara na ke so a ba ni. Ina da saurayi, yana so na, ni ma kuma Ina son shi, ga shi iyaye na sun matsa min akan na fito da miji nai aure. Ni kuma na kasa gaya mai yanzu haka wancan sati akai auren ƙanwata yanzu sun ce in ban fito da miji nan da wata ɗaya ba, duk wanda suka zaɓa min shi zan aura. Ni kuma Ina son wancan, amma na kasa gaya mai, kuma shi wanda nake so bai ban kosisin…
Read More