07
Oct
"Rashin ƙwaƙƙwaran abin yi bayan aure ne babban ƙalubalen mata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata na ba da gagarumar gudunmawa ga al'amuran da suka shafi cigaban al'umma, ta ɓangarori daban-daban. Daga ciki akwai mata da ke ba da gudunmawa a fagen harkar hidimar jama'a tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, suna gudanar da ayyukan jinƙai waɗanda jama'a da dama ke farinciki da su. Wannan agaji da taimako da ake bai wa waɗanda ke cikin halin tagayyara shi ya ja hankalin matashiya, Shamsiyya Ibrahim Barde, ýar garin Potiskum a Jihar Yobe ta shiga aikin hidimar al'umma, musamman bayan fitintinun da aka…
