Mata A Yau

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A makon da ya gabata na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta. Yanzu za mu ɗora daga inda aka tsaya a wancan mako. A sha karatu lafiya. Yanzu za mu daga inda muka tsaya a cikin jerin dalilan da wasu zawarawan suke kauce hanya. Ko na ce suke yin ayyuka na rashi kamun kai. *Rashin haƙuri: Wasu matan da ma Allah ya halicce su da ɗabi'ar rashin haƙurin iya zama ba…
Read More
Yadda za ki gyara nononki ta hanyar amfani da tumfafiya

Yadda za ki gyara nononki ta hanyar amfani da tumfafiya

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya ƙara mana lafiya da zaman lafiya. Da yardar mai kowa da komai, shafin Kwalliya na jaridar Manhaja na wannan makon zai waiwayi mata da ke neman hanyar gyara nonuwansu, kamar yadda muka sani a gyaran jiki, nono zai shiga a layin farko ga mata, kasancewar sa babban alama da ka iya bambanta mace da namiji, kuma kamar yadda matar manzoni rahma, Nana Aisha Allah Ya ƙara yarda da ita ta ce, gemu ne adon maza, yayin da nonuwa suke kwalliyar mata. Kenan gyara nono zai iya…
Read More
Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin kuyanga da ya siya

Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin kuyanga da ya siya

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba. Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu, sai a gidan…
Read More
Macen Arewa ba raguwa ba ce kamar yadda wasu ke faɗa – Ayat Uba Adamu

Macen Arewa ba raguwa ba ce kamar yadda wasu ke faɗa – Ayat Uba Adamu

"Wasu mazan na jiran matansu su samu ne su ba su" Daga AISHA ASAS Kamar yadda aka sani, matan Arewa sun yi fice wurin biyayyar aure, kula da 'ya'yansu tare da haƙuri da duk matsalolin da za su iya cin karo da su a gidan aure. Macen Arewa ce za ta miƙe haiƙan ta nemi na kanta, ta yi amfani da abinda ta samu a neman nata, ta girka abinci, ta ciyar da 'ya'yanta har ma da mijin idan yana tare da su. Macen Arewa ce za ta ɗora kaso mai yawa na buƙatun gidanta a wuyanta, tsayin lokaci, amma…
Read More
Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A wannan mako zan so na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta bayan rabuwar aurensu. Da farko dai wacece bazawara? Bazawara ita ce wacce ta rabu da mijinta ta hanyar sakin aure ko kuma wanda ya mutu, ko ma wanda ya vace. Ƙasar Hausa kamar yadda muke gani a halin yanzu, ta zama tamkar shalkwatar yaye ƙanana da manyan zawarawa har ma da dattijai. Ba sai na kawo dalilan da suke…
Read More
Burina shi ne kada na yi tarayya da ƙanena wurin dogaro da iyayenmu – Aisha Tanabiu

Burina shi ne kada na yi tarayya da ƙanena wurin dogaro da iyayenmu – Aisha Tanabiu

"Ina da burin samun mijin da zai bar ni na nemi na kaina" Daga AISHA ASAS  Neman na kai bai zama lallai sai ga macen da ta yi aure har ta haifafa ba, kamar yadda a shekarun baya a Ƙasar Hausa an fi ba wa sana'ar matar aure mai 'ya'ya muhimmanci fiye da ta matashiya mai shirin yin auren. Wataƙila hakan bai rasa nasaba da cewar, ita mai auren ta fi mallakar hankalinta, kuma ita ce ke da 'ya'ya da za ta nema don su amfana. Yayin da wasu ke ganin macen da ba ta yi aure ba ba ta…
Read More
Ta yaya rashin tsafta ke iya haifar wa mace ciwon sanyi?

Ta yaya rashin tsafta ke iya haifar wa mace ciwon sanyi?

Daga AISHA ASAS Tun a farkon darasin idan ba a manta ba, mun kawo a ɗaya daga cikin ma'anonin da ake yi wa ciwon sanyi da cewa, ciwo ne da ke samuwa sakamakon rashin tsaftace al'aura. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu yi sharhin waccan ma'ana, wato hanyoyin da rashin tsafta za ta iya haifar da cutar sanyi ga mata. Kusan kodayaushe a na huɗuba ga mata, akan yi kira gare su da su kula da farjinsu, su tsaftace shi, kuma kada su bar wurin da duk wani abu da zai gayyato masu ƙwayoyin cuta. Na san…
Read More
Yakamata iyaye da sarakuna ku daina kashe kes na cin zarafi a tsakaninku – Rabi Salisu

Yakamata iyaye da sarakuna ku daina kashe kes na cin zarafi a tsakaninku – Rabi Salisu

“Za mu tabbatar da ƙwatar wa marasa ƙarfi ’yancinsu” Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al'umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda kuma a dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a…
Read More
Alamomin da mata ke ji da ke tabbatar da suna ɗauke da cutar sanyi

Alamomin da mata ke ji da ke tabbatar da suna ɗauke da cutar sanyi

Daga AISHA ASAS Mai karatu barka da yau, barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja. Har wa yau dai muna kan darasin ciwon sanyi, wanda idan ba a shafa'a ba, mun faro ne daga bayani kan ma'anonin da ake yi wa ciwon sanyi, zuwa bayyana adadi da karkasuwar ciwon. A wannan satin da yardar mai dukka, shafin Kwalliya zai yi duba kan alamomin da mace za ta ji da za su iya tabbatar mata tana ɗauke da ɗaya daga cikin nau'ukan ciwon sanyi na mata. Hakan kuwa wata dama ce da za ta iya taimaka wa wurin…
Read More
Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Daga MUKHTAR YAKUBU  Gyara muhallin zama da kwanciyar sa ( palour da ɗaki)  Shirya masa abinci da abun sha a kan lokaci Tanadar masa da ruwan wanka  Tsara lokacin baccin yaranku Kimtsa jikin ki da amfani da turaren dare masu sanyi da kwantar da hankali ( dan Allah a kiyaye amfani da turare mai ƙarfi kamar na 'yan bori lokacin bacci, ana buƙatar abunda zai sa ma zuciya da ƙwaƙwalwa nutsuwa ne ba abunda zai hargitsa shi ya yi activating brain ɗin mutum ba)  In yana da gajiya a masa matsa/tausa mai sauke gajiya (a sa hankali a ƙeya, wuya,…
Read More