Mata A Yau

Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Hanyoyin da za ki samar wa miji hutu da nutsuwa idan ya dawo gida

Daga MUKHTAR YAKUBU  Gyara muhallin zama da kwanciyar sa ( palour da ɗaki)  Shirya masa abinci da abun sha a kan lokaci Tanadar masa da ruwan wanka  Tsara lokacin baccin yaranku Kimtsa jikin ki da amfani da turaren dare masu sanyi da kwantar da hankali ( dan Allah a kiyaye amfani da turare mai ƙarfi kamar na 'yan bori lokacin bacci, ana buƙatar abunda zai sa ma zuciya da ƙwaƙwalwa nutsuwa ne ba abunda zai hargitsa shi ya yi activating brain ɗin mutum ba)  In yana da gajiya a masa matsa/tausa mai sauke gajiya (a sa hankali a ƙeya, wuya,…
Read More
A da ne mata suka fuskanci ƙalubalai a aikin jarida – Khadija Salihu

A da ne mata suka fuskanci ƙalubalai a aikin jarida – Khadija Salihu

"Girki na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure" Daga AISHA ASAS Masu karatunmu Allah Ya kawo mu, sati ya zagayo, sannunku da ƙoƙarin bibiyar jaridar Manhaja. Shafin Gimbiya mai kawo maku fira da mata daban-daban kan sha'anin rayuwarsu, tun daga sana'o'insu ko ayyukan da suke yi, zuwa ƙalubalai da kuma nasarorin da suka samu. Shafi ne da ke ƙoƙarin ganin ya zama allon kallo ga mata, ta hanyar zaburar da su kan neman na kansu, taɓo ɓangarorin da za su share hawayen wasu mata su fahimci ba su kaɗai ne ke fuskantar matsalolin da suke ciki ba, kuma ilimi gare…
Read More
Za mu tabbatar da kwatar wa marasa ƙarfi ’yancin su – Hajiya Rabi Salisu

Za mu tabbatar da kwatar wa marasa ƙarfi ’yancin su – Hajiya Rabi Salisu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al'umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda a kuma dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a matsayin kwamishinar jinƙai ta jihar. Wakilin Blueprint Manhaja, MAHDI…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya ki ke. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a ƙirga don sanar da ke tawa damuwa saidai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi min mummunar fahimta. Wallahi tun 'last year' mahaifiyar 'best friend' ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita. Tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauka ta duk lokacin da babu karatu, ko mu je 'hotel' ko ta kai ni wani gida. To…
Read More
Da me matan banza suka fi na gida? (2)

Da me matan banza suka fi na gida? (2)

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinmu na zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A makon da ya gabata mun kawo muku maudu'i kan mai matan bariki suka fi matan aure har wasu mazan suke tsallake matansu na aure suna biye wa 'yan bariki? Mun fara kawo muku dalilai har guda 7. A yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya. Iya abinci: Matan wajen suna bai wa mazansu abinci. Wata ma a nan take wanke masa duk wani laƙani don mallake shi. Za ka ji namiji yana zancen abincin budurwarsa kamar…
Read More
Macen da ba ta da abin yi na saurin gundurar namiji – Aisha Adamu Sadiq

Macen da ba ta da abin yi na saurin gundurar namiji – Aisha Adamu Sadiq

"Wasu matan babu ce ke jefa su halin rashin kamun kai" Daga AISHA ASAS Masu azancin zance suna cewa, sana’a goma maganin mai gasa. A wannan makon shafin Gimbiya na jaridar Manhaja ta ɗauko maku matashiya mai sana'ar sarrafa fara, siyar da abayoyi, akwatuna da ma haɗa lefe bakiɗaya. A tattaunawar Manhaja da matashiyar, ta tavo yadda sana'ar siyar da fara ke bayar da abin rufa asiri, saɓanin yadda mutane da dama suke kallonta a matsayin shiririta. Sannan kuma ta yi ƙarin haske kan yadda sana'arta ta haɗa lefe ke gudana. Babban fatanmu dai mata su amfana da wannan shafin,…
Read More
Me ake cewa ciwon sanyi na mata?

Me ake cewa ciwon sanyi na mata?

Daga AISHA ASAS Idan aka ce ciwon sanyi, akan samu bambancin fassara daga mutane da dama, wanda ke kawo ruɗani, har matan su kasa bambance wane ne haƙiƙanin ma'ana ta wannan ciwo da ake wa laƙabi da na sanyi. Wasu da dama suna kiran ciwon sanyi a matsayin cuta da ake kamuwa da ita ta hanyar kwanciyar aure, inda suke bayanin ta a matsayin cuta da ake saka wa mata. Wasu kuwa suna fassara ciwon da cutar da ake samu sakamakon rashin tsaftace al'aura, kama daga rashin wanke kamfai akai-akai, rashin amfani da shi, rashin tsaftace wurin da abin da…
Read More
Dandalin shawara: Matata ba ta taɓa gode wa ƙoƙarina ba

Dandalin shawara: Matata ba ta taɓa gode wa ƙoƙarina ba

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Malama Aisha, sannu da ƙoƙari. Ya iyali? Allah ya yi jagora. Don Allah Ina so ki ja hankalin mata a shafinku na iyali akan mata masu ƙin gode wa mazajensu, wallahi wasu matan ba su da imani, ko kaɗan ba su aminta da matsalar rayuwa da ake ciki a yanzu ba. Matata shekara 10 muna tare, amma ban taɓa barinta da yunwa ba, ba a taɓa ranar da ban kawo ba, sai dai wata rana da daɗi wata rana ba daɗi. Ba ta taɓa gode ƙoƙarina ba, sai dai duk ranar da na kasa kawo irin…
Read More
Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

"Samarin yanzu ma sun fi son mace mai sana'a" Daga AISHA ASAS Mai karatu yau fa mun zo da abinda ba ku yada gani ba, mace da ta tabbatar da zancen ba sana'ar da namiji zai yi da mace ba zata iya ba matuƙar ta sa wa ranta za ta iya. A daidai wannan lokacin da mata suka miƙe, suka yi tarayya wurin kama sana'ar kayan qawa na mata da maza, kama daga tufafi, takalma zuwa huluna, gyale da sauransu, waɗanda su ne sana'oin da aka cika ganin mata na yi. A cikin haka ne, aka samu wata matashiya da…
Read More
Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

"Ilimin 'ya mace har mijinta ke amfana" Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Kamar kowanne mako, shafin Gimbiya na yi maku tanadi na musamman wanda muke da tabbacin mata za su amfana ta vangarori da dama, ya Allah ya zama ƙwarin gwiwa ga wasu, wasu ya zama ilimi da zai taimaka masu wurin miƙewa neman na kai, yayin da yake zama allon kwaikwayo don saisaita rayuwarsu bisa ga turba da za ta tsirar da su. A wannan satin, mun samu baƙuncin wata matashiya da ta ɗauki sana'a da muhimmanci, mai sana'ar 'yankunne ce,…
Read More