Dandalin shawara: Matata ba ta taɓa gode wa ƙoƙarina ba

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Malama Aisha, sannu da ƙoƙari. Ya iyali? Allah ya yi jagora. Don Allah Ina so ki ja hankalin mata a shafinku na iyali akan mata masu ƙin gode wa mazajensu, wallahi wasu matan ba su da imani, ko kaɗan ba su aminta da matsalar rayuwa da ake ciki a yanzu ba.

Matata shekara 10 muna tare, amma ban taɓa barinta da yunwa ba, ba a taɓa ranar da ban kawo ba, sai dai wata rana da daɗi wata rana ba daɗi. Ba ta taɓa gode ƙoƙarina ba, sai dai duk ranar da na kasa kawo irin wanda ta ke so idan ban kai zuciyata nesa ba sai kowa ya ji mu, don ta dinga tsiga da kushe abin da na kawo tare da masifa tamkar ban taɓa yi mata alheri ba. Don Allah mata ku ji tsoron Allah. Ku san Annabi ya kafu. Ku tausaya mana musamman a cikin irin wannan lokaci na taɓarɓarewar tatalin arziki. Allah ya saka da alhairi. Na gode.

AMSA:

A wannan zamani da mu ke ciki mata da yawa za su shiga wuta idan ba su tuba ba akan muzgunawa mazajensu da su ke yi. Saboda yawan ƙorafe-ƙorafen mata ya sanya ake ganin su ne suka fi cutuwa a zamantakewar aure, sai dai an ce “dokin mai baki ya fi gudu”. Da maza za su buɗe baki kamar yanda mata ke yi da mun aminta matan ma ba a bar su a baya ba wurin zama ba ‘yan goyo ba.

Akwai wa’ansu laifuka da tun a duniya muke girban su ciki kuwa har da butulcin mace ga mijin ta. Rashin godewa a abin da miji ya yi. ‘yar’uwa ki buɗe kunne da kyau ki ji ni, idan ba ki daina wannan ɗanyen aiki da ki ke yi ga mijinki ba, makoma biyu ce, kuma dole cikin biyu ki samu kanki a ɗaya. Ko dai wata rana ya gaji ya ƙyale ki tun da idan ma ya yi ba tsira ya yi ba. Ko kuma ya gaji, ya kora ki gidanku ki koma goro ko abin siyen shi. Ko ki auri wani mijin da zai gasa ma ki gyaɗa a hannu, ba ci, ba sha, sai wahala.

‘yar’uwa abin da ba ki sani ba, mijinki duk yanda ki ke ganin sa wawa, ko wanda bai san ciwon kansa ba don kawai yana kwanta ma ki, to zuma ne shi, yasan yanda ake harbi mai tsananin zafi, kuma ya iya shayar da zaƙin zumar idan ya so. Sau da yawa mu da kanmu muke mayar da mazajenmu abin da muke kuka da ƙorafi kai.

Ke kin samu yana kawowa ko ba daɗi, wata na can ita ke fita ta nemo, ta ciyar da ‘ya’yanta da kanta, ba wai don ba ta da miji ba, sai don ya qi ciyar da su, ko dai don yana maƙetacin miji, ko don ya ji ba zai iya fita ya nemo ba.

A wannan lokaci da muke ciki maza masu riƙe cin iyalansu wallahi sun yi qaranci, don haka abin da ki ke yi ba komai ba ne face butulcewa ni’imar da Allah ya yi ma ki. Tun wuri ki farka, tun ba ki janyo wa kanki fitinar da za ta ƙare kanki ba.

Mata ku ji tsoron Allah.! Ku taimake mazajenku a cikin wannan yanayi na matsin rayuwa. Ku yi masu uzuri a akan gazawar lalurorinku. Sannan ku roƙa masu Ubangiji ya ba su su ba ku. Lallai wanda ya gode Allah zai ƙara masa.