Shin waye bai taɓa sauya sheƙa ba?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Sheƙa dai da duk wanda ya fahimci sunan na nufin ‘Gidan Tsustsu” da ya kan gina ko sassarƙafa da kan sa cikin baiwar da Allah ya yi ma sa. Haƙiƙa tsuntsaye na da basirar gasken gaske don yadda su kan saka sheƙar nan su kaɗai. Za ka ga wasu tsuntsayen na tafiya wani waje su na ɗauko kayan haɗa sheƙa ɗaya bayan ɗaya su na sagalawa har su gama. Kwanan nan naga wani hoto mai ban tausayi da ke nuna ’ya’yan wata tsuntsuwa sun mutu a cikin sheƙa sai a ka rubuta ba mamaki an kashe mahaifiyar su ne.

Sheƙar akwai babba bisa girman tsuntsun akwai kuma karama nan ma bisa girman tsuntsun. Tsuntsaye kamar kabari na yin sheqa da dama a kan bishiya daya wato kowa da gidan sa. Jemagu da alallaƙa ma na da irin ta su shekara. Za ka ga wasu tsuntsaye na maƙalewa a jikin kangayen gidaje wasu kuma na shiga cikin ramukan rufi su na mai wajen gidan su. Duk wannan shimfiɗa ce ta asalin yadda sheka ta ke kafin mu shigo batun sauya sheƙar ’yan siyasar Nijeriya.

A ƙasashen da dimokraɗiyya ke da tushe irin Amurka da Burtaniya ’yan siyasa kan zauna a sheƙar jam’iyyar su har ƙarshen rayuwar su. Ba mamaki hakan na nuna tsarin su ko muradun su su na nan a rattabe a kundin mulkin jam’iyyun kuma a kan bi muradun sau da kafa. Za ka samu ɗan siyasa na wakiltar jam’iyya sa a majalisar dokoki na tsawon shekaru aru-aru har rai ma ya yi halin sa ko tsufa ya sa a koma gefe don bar wa masu sauran kuzari su dora daga inda a ka tsaya.

Bisa tsarin mulkin ƙasashen kowa na da ’yanci a cikin su ya shiga jam’iyyar da ya ke so amma za ka ga in sun shiga jam’iyya shikenan sun zauna ba guguwar da za ta sauya sheƙar su. A nan Nijeriya ma an yi irin hakan ai a farkon mulkin ’yan ƙasa wato jamhuriya ta farko da sojoji su ka kawo ƙarshen ta a ranar 15 ga watan Febreru 1966 inda a ka yi kisan gilla ga firaminista na farko kuma na ƙarshe zuwa yanzu Sir Abubakar Tafawa Balewa, firminiyan kudu maso yamma Chief Ladoke Akintola da firamiyan Arewa Sir Ahmadu Bello. Wataƙila da waɗancan jam’iyyu da su ka faro daga NPC da ta fara ɗarewa kan karagar mulki sun ɗore da za a iya dasa irin wancan ɗabi’ar ta zama a jam’iyya ɗaya.

Hakanan ma a jamhuriya ta biyu inda a ka samu jam’iyyu irin NPN, UNPN, PRP, GNPP da sauran su an buga siyasa sosai inda kowa ya tsaya tsayin daka kan jam’iyyar sa. Duk da wa’adi na farko da a ka samu daga 1979 zuwa 1983 ya gama lafiya amma wa’adi na biyu ya samu tarnaƙi daga soja inda shugaba Buhari ya na soja a lokacin ya zama shugaba gabanin abokan sa sojoji su kifar da gwamnatin sa har a ka yi ta mulkin sojojin zuwa 1999.

Duk wanda ya duba tarihin siyasar Nijeriya daga 1999 zuwa yanzu zai amince sauya sheƙa daga PDP zuwa wata jam’iyya ko ma a dawo PDP gabanin zaɓen 2015 ba wani abun mamaki ba ne. Daga nan kuma a ka samu APC inda don ɗan siyasa ya bar jam’iyyar sa ya dawo APC ba mamaki. Wasu ma kan fita daga APC don tsayawa takara da zarar sun lashe sai su nemi dawowa gidan su na tsamiya.

Wani lokacin kuma ba lalle ba ne sai an samu lashe zaɓe. Wani dan siyasa in ya gwada qarqashin wata jam’iyya ya ga ba nasara sai ya sake dawowa APC ko ya koma PDP. Yanzu kuma ga shi ma sanadiyyar zaɓen 2023 an samu zaɓin LP da NNPP ga ma tsohuwar jam’iyyar SDP ta samu farfaɗowa.

Masana kimiyyar siyasa sun duba dalilan sauya sheƙar inda su ka fi ƙarfafa cewa duk aqidar jam’iyyun iri ɗaya ne, wato ma’ana a kan rubuta manufofin a kan takarda amma babban burin shi ne lashe zaɓe ta kowane hali da kuma maƙalewa a kan mulki ko da ba a taɓuka abun kirki. Wataran ku gwada tambayar wani ɗan siyasa rubtattun manufofin jam’iyya s aka sha mamaki. Don haka babbar jam’iyya ko jam’iyya mai gwamnatin tarayya ta fi samun masu marmarin shiga don ko dai ba su lashe zaɓe ba za su iya samun wajen maƙalewa.

Wani dalilin wanda ya ke zaman raɗe-raɗi shi ne neman kariya daga laifukan da a ka tafka inda aƙalla an ji tsohon shugaban wata jam’iyya na cewa in dai a ka dawo jam’iyya sa to an huta daga tsangwamar hukumar bincike. Wani dalilin da yanzu ya fara sanyi shi ne gujewa zama a jam’iyya marar rinjaye don rasa samun gatar da ’yan jam’iyya mai rinjaye kan samu daga tarayya.

Canjin ya faru ne bisa dalilai biyu. Na farko za ka ga gwamna a jam’iyya adawa amma rawar da ya ke takawa wajen kare muradun jam’iyya mai ci kan iya shallake na gwamnan da ke cikin jam’iyyar. A gwamnatin da ta shuɗe an ga wasu gwamnoni da ke da tagomashi wajen shugaban ƙasa fiye da wasu gwamnonin jam’iyya don iya abun da a ke cewa taku. Dalili na biyu shi ne yanda jama’a masu zaɓe kan iya zabar wanda su ke so ba tare da la’akari da jam’iyya da ya tsaya takarar ba.

Misali a fili shi ne Ahmad Aliyu Wadada a mazaɓar tsohon shugaban APC Abdullahi Adamu wato Nasarawa ta yamma da ta haɗa da ƙaramar hukumar Karu, Keffi, Kokona, Nasarawa daToto. Wadada ya so ya yi sulhu da Abdullahi Adamu don samun tikitin majalisar dattawa a APC amma hakan bai samiu ba don haka Wadada ya sauya sheƙa zuwa SDP kuma ya lashe zabe. Kujerar nan fa ita ce wacce Abdullahi Adamu ya sauka daga kan ta lokacin da ya zama shugaban APC.

Ga mazabar ɗan majalisar dattawa na Abuja inda al’ummar Gwarawa masu rinjaye kan zavi ɗan uwan su Philip Tanimu Aduda a tsawon shekaru amma a zaɓen da ya gabata sai su ka sauya da zaɓar Ireti Kingibe ta jam’iyyar LP a kujerar. Ba shakka hakan ya ba wa Aduda mamakin gaske duk da zargin wasu dalilai daban da su ka jawo hakan.

Magoya bayan jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso sun ce jam’iyyar ba za ta daina tasiri ba matuƙar jigon na su na cikin jam’iyyar.

Wannan ya biyo bayan hukuncin kotun zaɓe a Kano da ta ba wa APC nasara da kuma ja da baya da wasu ‘yan jam’iyyar su ka yi da zummar sauya sheƙa zuwa APC. Dama da yawa daga cikin su ma ’yan APC ne a baya da bacin rai ya sanya su ka kauce zuwa inda su ka ɗauka ya zama tamkar tudun mun tsira.

NNPP wacce gabanin babban zaven 2023 ba ta da wani babban tasiri; ta zo ta 4 da mafi yawan quri’a kazalika da samun kujerar gwamna da ‘yan Majalisar Dattawa da wakilai da kuma a matakin jiha musamman za a ce Kano kenan.

Haƙiƙa tasirin jam’iyyar na da nasaba kai tsaye da siysara tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Jigon jam’iyyar Injiniya Buba Galadima ya zayyana Kwankwason da zama mafi tasiri a tsakanin ‘yan siyasar arewacin Nijeriya. Galadima ya ce ya sha fadar fifikon Kwankwaso kan sauran ’yan siyasar Arewa amma ba wanda ya tava ƙalubalantar sa.

A na sa matakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a Bauchi Sanata Halliru Jika wanda ya koma APC ya ce ya shaidawa Kwankwason matakin da ya ɗauka kuma ya ce ba don wani alƙawari ko neman wani mukami ya sa shi sauya sheƙar ba. Jika ya ce ya na da bayanin Kwankwaso ma don alakar sa da shugaba Tinubu zai iya komawa APC.

Duk da manyan jam’iyyun adawa PDP da LP na kotun ƙoli don ƙalubalantar nasarar Tinubu, mai ba da shawara kan siyasa Ibrahim Masari na nanata kiran rage hamaiya har zuwa kakar wani zaɓen.

Sauya sheƙa a siyasar Nijeriya ba wani sabon abu ba ne don misalin shugaban majalisar dattawa na yanzu Godswill Akpabio wanda ya taba zama shugaban marar sa rinjaye na majalisar a lokacin ya na PDP har ma ya taɓa jagorantar ’yan uwan sa ’yan PDP su ka yi tawaye ta hanyar ficewa daga zauen majalisar a na tsakiyar zama; ya shige APC a mulkin Buhari ba tare da yi wa PDP karin haske ba. Shigewar ta sa ta samu la’ada da zama babban ministan Neja Delta yanzu kuma ga shi shugaba Tinubu ya yi uwa da makarbiya sai da ya tabbatar Akpabio ya zama shugaban majalisa.

Kammalawa;

Mai ɗaki shi ya san inda ke ma sa yoyo don haka ya dace masu zaɓe su riƙa ɗaukar siyasa da sauƙi ba tare da zundumawa juna ashar don neman kare gwanayensu ba A fili akasarin ’yan siyasar Nijeriya na shiga siyasa ne don samun madafun iko su rika sukuwa a kan dukiyar talakawa. Jama’a su riƙa siyasa mai tsabta da neman duk wanda zai yi takara ya kawo manufofin sa a rubuce a yi yarjejeniya ya rantaba hannu don aƙalla hakan ya zama shaida tun a duniya.