Me ake cewa ciwon sanyi na mata?

Daga AISHA ASAS

Idan aka ce ciwon sanyi, akan samu bambancin fassara daga mutane da dama, wanda ke kawo ruɗani, har matan su kasa bambance wane ne haƙiƙanin ma’ana ta wannan ciwo da ake wa laƙabi da na sanyi.

Wasu da dama suna kiran ciwon sanyi a matsayin cuta da ake kamuwa da ita ta hanyar kwanciyar aure, inda suke bayanin ta a matsayin cuta da ake saka wa mata.

Wasu kuwa suna fassara ciwon da cutar da ake samu sakamakon rashin tsaftace al’aura, kama daga rashin wanke kamfai akai-akai, rashin amfani da shi, rashin tsaftace wurin da abin da ya dace, ko rashin tsaftar ban ɗaki da ababen da ake tu’ammali da su a ciki, da dai sauransu. Ma’ana dai cuta ce da ke samuwa sakamakon ƙwayar cuta da ake samu a muhallin da dauɗa ta wanzu.

Fassarar ciwon sanyi a wasu wuraren kuwa shi ne, yi wa farjin kutse ta hanyar amfani da ababen da ba su dace da muhallin ba, kamar wasu da yawa daga kayan mata da ake cusawa a wurin ba tare da sanin inganccinsu ba, ko yawan tura farce ba tare da an yi la’akari da tsaftarsa ba, ko sanya turare musamman waɗanda aka yi ba don wurin ba, da makamantansu.

A wani ɓangaren akan fassara cutar sanyi da ƙwayar cuta da ke fita ta dubura wadda a bisa rashin kulawa kan sa su dawo farjin mace, ya Allah ko ta sanadiyyar fara wanke bayan kafin gaban, har hannun ya kwaso ta zuwa gaban, ko ta hanyar gangarowar ruwan wanke bayan waɗanda ke ɗauke da ƙwayar cutar zuwa farji, da dai makaranta su.

A wani wurin cutar sanyi na nufin cutar da ake samu idan ana yawan shan magunguna na kashe ƙwayoyin cuta, wato abinda ake kira da ‘antibiotics’ a turance. Saboda yawaitar sa na kashe ƙwayoyin cuta da ke da amfani ga farjin mace, wanda suke yaqi da ƙwayoyin cuta da ke haifar da ciwon sanyi, abinda masana ke kiran su da nomal fulora (normal flora).

Akwai kuma masu cewa, ciwon sanyi na samuwa idan wasu cutuka na ciki, kamar ciwon suga, samuwar juna biyu, da duk wata cuta mai karya garkuwar jiki.

Abin tambaya anan shin wacce fassara ce daidai?

Za mu ci gaba.