Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya ki ke. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a ƙirga don sanar da ke tawa damuwa saidai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi min mummunar fahimta. Wallahi tun ‘last year’ mahaifiyar ‘best friend’ ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita.

Tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauka ta duk lokacin da babu karatu, ko mu je ‘hotel’ ko ta kai ni wani gida. To matsalata dai Ina jin tsoron ‘friend’ ta san abinda mu ke yi. Don yanzu har gidanta ta ke zuwa da ni. Ina neman shawarar yadda zan daina dan Allah Ina son ‘friend’ ɗita, na san zan rasa abotamu duk ranar da ta san abinda na ke yi da mahaifiyarta. Dan Allah mummyna ki ba ni shawara.

AMSA:

Da farko dai ba zan faɗi abin da ki ke son ji ba, wato laifin dukka na mahaifiyar ƙawarki ne ba, kasancearki mai ƙarancin shekaru, ta yi amfani da yarintarki wurin sanya ki abin da ba ki da ra’ayi. Idan na gaya ma ki hakan na yi ma ki ƙarya, duk da cewa ta fiki laifi, hakan ba yana nufin ba ki da laifi ko kaɗan ba.

Abota na nufin amana, kuma ita amana ba a shekaru ta ke ba, ba ta da wani sharaɗi da sai ka kai shi ake tsamanin samun ta a tare da kai. Idan har kin kasance mai sanin ya kamata, bai kamata da hankalinki ba ƙarfi aka yi amfani da shi wurin tursasa ki ba ko wani abin maye ba ki iya amincewa da mahaifiyar abokiyarki ta amana a irn wannan mu’amala.

Abin da ya kamata ki fara tambayar kanki a lokacin da ta nuna ra’ayinta kanki, ya ƙawata za ta ji idan na aikata hakan da mahaifiyarta? Wane irin hali zata tsince kanta? A zuciyarki ki yi musanyar wuri da ita, ma’ana ki tambaye kanki idan ke ce mahaifiyarki ta nemi hakan da ƙawarki ya za ki ji? Amsar da ki ka ba wa kanki ce ya kamata ki yi amfani da ita wurin yanke hukunci matuƙar ba ki kasnce a cikin mutane masu son-kai ba.

A taƙaice abin da ki ka aikata tsabar son kai da rashin amana da ki ke da shi ne ya jagoranci wannan ɗanyen aiki da ki ka yi, don haka sai kin fara da amincewa da su tare da ɗaura aniyar canzawa ne duk wani abu zai iya yin tasiri.

Idan na koma ɓangaren iyaye, zan iya cewa kamar kullum muna da kaso a mafi yawan ayyukan da ‘ya’yanmu ke aikatawa. Wannan ne karo na kusan huɗu ko biyar da na samu irin wannan neman shawara duk da cewa suna da mabambantan tushe da asali, amma dukkansu sun tafi kan matasan ‘ya’ya da suka faɗa mumunar hanya ta sanadiyar sha’awa.

Sha’awa hallita ce kamar yadda tsari da zubin jikin ɗan adam yake. Kowa da irin yadda aka hallita masa tasa, akwai yaron da ya turo min da saƙon neman shawara, mai shekaru 15, yana sanar da ni yana da ƙarfin sha’awa da har manyan mata birge shi suke, sai dai har zuwa lokacin iyayenshi na haɗa shi kwanciya da ‘yan’uwanshi mata ko baƙi mata idan suka zo.

Ba kuma don babu wadatar muhali ba, wai saboda tursasa zuciyarshi amincewa da har lokacin shi yaro ne, kuma yana da doguwar tafiya kafin ya kai ga zancen aure. Abin takaici mahaifiyarshi ta yanke wannan hukuncin ne a lokacin da ta kama shi yana roƙon mai aikinsu ta bari ya tava ta zai bata dubu ɗaya.

Sannan mahaifiyar wani yaro ɗan shekara 19 ta neme ni kan sha’anin matsalar ɗanta da ita ta ɗora ta a vangaren taɓin hankali. Yaron idan ana biki ko wani taro na dangi, yakan zauna ne a ɗakin da ‘yan matasan mata ke zama na daga dangi da abokan arziki, amma fa mafi yawan su sun girmeshi. Matuƙar babu iyaye a ɗakin to zai dinga ciro al’aurashi a gaban su.

Abin tun matan na haƙuri har suka fara faɗa da shi, har aka fara kawo ƙararshi ga mahaifiyar ta shi. A taƙice dai bayan dogon zama da tataunawar da na yi da yaron na fahimci ba wata hauka face tsabagen sha’awa da ke cin shi. Ƙarancin shekarunshi ya sa yake ganinta wannan hanyar zai iya samun wadda za ta kulashi.

Abin da zai ba ku mamaki shi ne, yaron da kansa ya nemi mahaifiyarshi ta yi masa aure ko da a cikin gadon da ya gada daga mahaifinshi ne, ita kuwa ta tabbar ma shi sai ya kammla karatun jami’a kuma ya fara aiki ko kasuwanci.

A nan ba wai ina son in nuna illar ƙin yi wa yaron da bai da sana’a aure ba. Tabbas wannan ce hanya mafi daidai, asalima abin kula da mata na daga ɓangaren ciyarwa da tufatrwa na daga cikin sharuɗan aure, sai dai iyaye su sani ba akan kowanne yaro wannan sharaɗi yake hawa ba.

Yana da kyau mu yi wa ‘ya’yanmu hukunci daidai da yanayi da halittarsu. Masu iya magana na cewa, wai ɗaurowa take a ɗaure alqali. Idan kin lura da irin halittar da ɗanki ko ‘yarki ke da ita ta ɓangaren sha’awa, ki daure ki yi masu hukunci daidai da ita.

Yawaitar sha’awar yaronki za ta sa ki karya tsarin da ki ka yi masa na rayuwa don kuɓutar da shi daga hallaka. Kuma yin hakan ba zai hana ki ɗora shi kan tsarin ba bayan kin samar masa nutsuwa.

A wannan zamani ‘yan mata da samari da yawa suna ajiye kunya su sanar da iyayensu aure suke so ayi masu, amma sai iyayen su kawar da kai daga hakan, kuma fa basa so su janyo mu su abin kunya, musamman ga ‘ya mace. Ta yaya ki ke tsamanin yarinyar da ta ajiye kunya ta sanar da ke irin sha’awar da ta ke da ga aure ta iya riƙe kanta tsayin shekarun da ki ka ɗibar mata na kammala karatu, ai sai wani tsari da Ubangiji.

Kuma sha’awa na ɗaya daga cikin ababen da masana halittar ɗan adam suka tabbatar na tava wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke da alaƙa da fahimta ko ajiyar abu, kamar karatu. Wannan kawai zai iya hana yara mayar da hankali kan karatun da kuka tura su yi a makaranta.

Don haka idan kuna da halin yi wa ‘ya’yanku maza aure, ku daure ko yi masu, daga baya su koma kan karatu ko sana’ar da za ta kula masu da gidansu. Idan kuwa babu, ku nuna masu hanyar nema, su nemo, su kawo, ku shige masu gaba kan aura masu matan da suka dace.

Kuma abin da b ku sani ba, shiryayyu daga cikin ‘ya’ya ne kawai ke damuwa da sai kun yi masu aure, saboda a wannan zamani akwai hanyoyi da dama da yara komai ganin da ku ke masu a matsayin yara za su samu yadda za su yi shashanci.

Misali ƙarami idan kana shawagi a kafar Facebook kawai za ka ci karo da shashanci da hanyoyin haɗuwa don gudanar da alfasha ba adadi. Akwai wata yarinya da ta tabbar min akwai wani zaure da ake masu tayin yadda ƙananin yara za su samu damar yin mu’amala.

Idan kana da ƙarancin shekaru kuma kana son ka yi, za ka turo da dubu ɗaya kacal, shi wannan sheɗanin ne zai samar ma abokiyar mu’amala a cikin yara ƙanana mata ko manya da ke da sha’awar lalata ‘ya’yan wasu. Shi ne zai samar ma ku wurin da za ku haɗu idan kana cikin Arewacin Nijeriya, (idan ƙananin yara ne kuwa da manya zai haɗa ku zai shirya wa mace har irin ƙaryar da za ta yi ta fita idan akwai tsauri a gidansu).

Karatu bai hana aure kuma aure bai hana karatu, don haka ku yi abinda ya dace don sauke haƙƙin ‘ya’yan da aka ba ku kiyon su.

Abu na gaba, idan na fahimce ki kina son hanyar da za ki bi don nisanatar wannan ɓarnar. To hanyar tuba na da sauƙi kuma tana da wahala, sauƙinta idan har a ranmu muna son tuban, hakan zai sa mu ƙyamaci abin da mu ke aikatawa da ba daidai ba.

Shawarata gare ki tana da matakai; da farko ki sanar da ita ba ki da ra’ayin ci gaba da wannan mu’amala, ki guje amsa kiranta idan ta buqaci haɗuwarku, idan ta matsanta ki yi barazanar sanar da ‘yarta abin da ku ke yi, idan duk ba su yi aiki ba, to hanya ta ƙarshe ita ce sanar da iyayenki su shiga tsakaninki da ita, ba zan ce dole sai kin yi hakan ba, saboda ban san yanayin naki iyayen ba, amma sau da yawa iyaye na nasarar raba ‘ya’yansu da waɗanda ke cin zarafinsu ta kowacce irin fuska kuma ba tare da sun tona asirinsu ba saboda kasancewarsu ‘ya’yansu.

Ba na jin waɗannan hanyoyin za su kasa bayar da sakamakon da ake buƙata, sai dai idan har na ƙarshen zai yi ma ki wahala wataƙil saboda irin iyayen da ki ke da su, to akwai wasu amintattun malamai da mu ka fara ƙulla alaƙa da su a wasu jihohi na Arewacin ƙasar nan, duk da zuwa yanzu ba su da yawa, Sakwatto, Kano, Kaduna, Abuja, Jos da kuma Nasarawa.

Muna amfani da waɗannan malaman a sha’ani na rikicin aure da iyaye da ke buƙatar dole sai an shiga tsakani fuska da fuska, ko karɓar Musulunci da sauran matsalolin da ke buƙatar ido da ido.

To idan kina daga cikin garurukan da mu ka lissafo, zai iya zama hanyar da za ki iya bi, domin za su iya shiga a lamarin har kuma ta kai ga su da kansu su neme ta, hakan zai iya kawo ƙarshen lamarin.