‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

Bayanai daga Jihar Zamfara sun ce mutum 10 sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai kan wasu motoci a hanyar Magami zuwa Gusau a ranar Asabar.

An ce yayin harin, mahara sun ƙona motoci guda uku kana sun yi awon gaba da wasu fasinjoji da dama.

Manhaja ta kalato cewar harin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana a yankin Dogon Tsauni a daidai lokacin da motocin ke hanyarsu ta zuwa Gusau daga Magami.

Jaridar Premium Times ta ce an kwashi waɗanda suka ji rauni yayin harin zuwa babbar asibitin tarayya FMC da ke Gusau, babban birnin jihar, sannan an kwashi gawarwakin zuwa ɗakin adana gawarwaki na asibitin.

Wani malamin jinya a asibitin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “Mun kwashi gawarwaki guda 10 zuwa ɗakin adana gawarwaki jiya (Asabar). Biyar daga cikinsu ‘yan banga ne.”

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Yazeed Abubakar, bai amsa saƙon kar-ta-kwana da aka aike masa don jin ta nakinsa kan batun ba.