23
Nov
Daga AISHA ASAS Ɗaya daga cikin dama da ‘yancin da dokar Nijeriya ta bai wa mata akwai damar riƙe madafun iko, wato fitowa takara ta kowanne ɓangare, babba da ƙaramin muƙamai, tun daga shugaban ƙasa har zuwa kansiloli. Wannan ne ya sa jajirtattun mata da dama suka yi yunƙurin ɗarewa ɗaya daga cikin kujerun da za su ba su damar baje irin ta su hikima ta hanyar juya sitarin wani vangare na wannan ƙasar ko ƙasar bakiɗaya. Ba ɓoyayyen abu ba ne irin yunƙurowar da mata suka yi kan sha’anin da ya jivinci siyasa, sun sanya jajircewa da zata sa…
