Ina daga cikin mutanen farko da su ka kafa Kannywood – Zainab Ahmad

Hajiya Zainab Ahmad mace ce mai kamar maza kuma ‘yar gwagwarmaya da fafutikar nema wa marasa ƙarfi ko galihu haƙƙin su a wajen waɗanda su ka tauye ma su haƙƙin, da kuma kiraye-kiraye ga Gwamnati da tunasar da ita akan haƙƙin da ya rataya a wuyan ta, musamman ma a Arewacin Nijeriya inda ake fama da matsanancin rashin tsaro. Hajiya Zainab Ahmad ta yi fice a ɓangaren ayyukan agaji da taimakon al’umma wajen shige musu gaba don kwato ‘yancin su. Ga dai hirar da wakiliyar Manhaja ta yi da ita:

Daga AISHA ASAS

Mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.
Suna na Zainab Ahmad da aka fi sani da Bint Hijazi a shoshiyal midiya. Asalin mahaifi na ɗan Fagge ne, mahaifiya ta kuma ’yar Ƙofar Mata ce a cikin Jihar Kano. Aiki ya kai mahaifan mu Gusau, Jihar Zamfara a shekarar 1968 ko 1969, inda anan aka haife ni. Na fara Furamare a Gusau, daga baya na koma Kano sannan na sake dawowa Gusau (daliin rufe makarantar Furamare ta kwana a shekarar da aka yi a wancan lokacin). Daga nan na fara WATC Gusau, sannan na koma GGSS Kabo na gama JSS ɗina, sannan na wuce Girls Science Secondary School Taura Kano (Yanzu Jigawa) na yi SSS ɗina a can. Bayan na bar Taura na yi Difloma a Digital Computer School a Kano kafin na koma koyon kwamfuta a Bayero na yi course na wata 3, sannan na koma FCE Kano na yi ƙarama da babbar difloma. Ina daga cikin mutanen farko da su ka kafa masana’antar Kannywood inda na ke ɗaukar nauyi da rubutu. Ina  taɓa kasuwancin kayan ƙawa, atamfofi, leshina, kayan kicin. Ina kiwo sannan akwai turaren wuta da na ke yi.
Ina cikin mutanen da su ke  yaƙin nema wa marasa gata haƙƙi, da fafutukar neman gwamnati ta yi ƙoƙarin kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a Arewa da ma Nijeriya bakiɗaya (amma na fi karkata da yanki na Arewa.) Wannan kaɗan daga cikin abubuwan da na ke yi kenan.

Akan ce mace ’yar zaman gida ce, wanda maza kan fake da wannan kalmar su hana matan su neman na kan su, me za ki ce kan wannan?
Gaskiya ban amince da hakan ba, kuma tun ina ƙarama na ke sana’ar siyo kaya daga Kwatano da Togo ina sayarwa; ke har alewar madara na sayar lokacin ina Furamare

A matsayin ki ta mace mai sana’ar saye da sayarwa waxanne irin ƙalubale ki ka sa mu a sana’ar?
Amsar kaya bashi da kuma biya kaɗan-kaɗan na daga cikin matsalolin da na fuskanta. Sannan ina son yawan kyauta, wanda hakan ma  matsala ce sosai yawan kyauta

Nasarori fa?
Gaskiya na samu nasarori a cikin harkoki na mara misaltuwa, babu abinda zan ce sai godiyar Allah.

Wace kala ki ka fi so?
Ina tsananin son ruwan ɗorawa wato yellow, da kuma pink

Me ya fi birge ki?
Daraja ɗan Adam a kowane irin yanayi

Me ke saurin ɓata miki rai?
Munafurci da tozarci ga mutum komai ƙanƙantar sa. Sai kuma rashin adalci ga mara gata

Mu koma vangaren iyali, akwai?
Aure na ya mutu a shekarar 2016, ina kuma da yaro guda ɗaya.

Wane irin kaya ki ka fi so?
Ina son ɗinkin boubou ko dogayen riguna na atamfa, boyal ko yaduka marasa nauyi.

Wace shawara za ki ba wa mata da su ke zama a gida ba tare da sana’a ba?
Ina roƙon ’yan uwa na da su dage da sana’a komai ƙanƙantar ta. Wannan zai ƙara mana martaba da mutunci a ko’ina. Ina so su fahimci Allah ne kaɗai ba ya gajiya da ba kai.

Shin a na ki ɓangaren, namiji ɗan goyo ne?
Toh! Ya danganta; akwai mazan da su ka cancanci goyo har da majanyi, akwai kuma waɗanda ba su dace da kyautatawa ba.

Me ye dalilin ki?
Akwai matan da na san su na zaman lafiya da mutunta juna, kuma su na ƙoƙarin kyautata wa matayen su. Akwai kuma waɗanda na san su na zaman baƙin ciki da tozarcin mazajen su. Allah sa mu dace.

Me ki ka fi sha’awar yi a lokacin hutawar ki?
Karatu ko kallon fina-finan tarihi da na ban dariya. Amma na fi son karatu

Wane abinci ki ka fi so?
Tuwon dawa miyar kuka

A matsayin ki ta mace mai kishin Arewa, shin ta yaya ku ke wannan aikin na yaƙin neman haƙƙin marasa gata?
Zan ba ki misalin wanda mu ke kai a  yanzu, na wasu matasa 24 da su ka sayi takardun aikin ‘yan sanda akan naira 700,000, aka tura su garuruwa daban-daban, da aka tashi sai aka kama su aka kulle, amma manyan da su ka karɓi kuɗin ba a kama su ba. Alhamdu lillahi! Mun yi gwagwarmaya kuma mu na kan yi.

Shin kwalliya ta na biyan kuɗin sabulu a gwagwarmayar da ku ke yi?
Sosai ma kuwa! Domin cikin kashi 100, zan iya cewa mun samu nasara kamar kashi 30. Kuma mu na addu:a, kuma a tsaye mu ke qyam don faɗin gaskiya ko akan ko wane ne.

To masha Allah, Hajiya mu na godiya ƙwarai
Ni ma na gode.