12
Oct
“Shirin 'Mata A Yau' ya canza rayuwar iyalai da dama” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Hajiya Halima Ben Umar ba ɓoyayye ba ne a gidaje da dama na Nijeriya da maƙotan ƙasashe, musamman inda ake amfani da harshen Hausa, saboda rawar da ta ke takawa wajen gabatar da shirin ‘Mata A Yau’, wanda tashar talabijin na Arewa 24 ke gabatarwa. Tsohuwar ’yar jarida, ýar gwagwarmaya, kuma uwa, wacce gudunmawarta a harkokin cigaban al'umma ya ratsa birane da ƙauyuka, kuma har yanzu ta ke nuna kishi da jajircewa wajen faɗakar da ýaýa mata muhimmancin inganta rayuwarsu da ta iyalinsu. Wakilin Blueprint…
