11
Jan
"Matsalar ƙwaƙwalwa cuta ce da ba a fiya damuwa wajen magance ta ba" "Ana yi wa matsalar ƙwaƙwalwa gurguwar ma'ana" Daga ABUBAKAR M. TAHEER Hajiya Saratu Garba Abdullahi ƙwararriya malamar jinya ce wadda ta ke koyarwa a Tsangayar Koyon Aikin Jinya na Jami'ar Bayero dake Kano. Sai dai a halin yanzu ta ke Ƙasar Amurka tana digirin na uku, wato PHD, kan Nursing Research. A cikin wannan tattaunawa ta musamman da ta yi da wakilin Manhaja a Haɗeja, ta kawo irin matsalolin dake damun ƙwaƙwalen mutane, waɗanda ke sanadin faɗawa a babbar matsala ko aikata aikin danasani ba tare da…
