Dandalin shawara: Matana sun zame min ɓeraye a gida

Manhaja logo

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Malama Aisha sannu da ƙoƙari, ya kwana biyu. Ina ta bibiyar links ɗin da ki ke ɗorawa a ‘status’ na shawarwari da mata ke biɗa da ma ‘yan rubutun shawarwari ga mata. Shi ya sa na ce bari na neme ki don Allah ki yi amfani da damar da ki ke da ita ki ba wa mata shawara kan yi wa mazajensu sata da suka maida ba komai ba. Ai kin san matana biyu ne, amma sun zame min yadda ki ka san ɓeraye, ba halin in aje wando ko riga da ‘yan canji, sai a yi masu rabtau. Kuma an rasa zakara cikinsu, har riga-riga suke yi wurin wawushe ni, kuma kowacce ka tambaya sai ta nisanta kanta da laifin ko ta ɗora abin kan abokiyar zamanta. Wallahi ta kai yanzu indai Ina da kuɗin kirki a jikina, sai na samar masu makwanci kafin in shiga gida. Wani lokacin har sai na koma har gidan Innah na bata ajiya, sannan da safe idan na je dubata in karɓa. Don Allah ki ja masu kunne sosai, ki kuma nuna masu illar aikatawa, don na lura ba su san hukuncin abin ba, saboda abokanaina biyu na ƙorafi irin wannan duk da cewa nasu bai kai irin na nawa gidan ba, son tasu matar ɓerar gida ce, irin ɓeran nan ƙanana masu shegen tsoro da sun ga mutane su ɓace kamar walƙiya. Amma ni nawa sai dai a kira su da ɓeran Chana, manyan nan masu mugunyyar ɓarna.

AMSA:

Idan har ka tabbatar ka wadata iyalanka yadda Allah ya huwace ma ka. Idan na ce nauyin iyalanka ba kawai Ina nufin tabbatar da tukunyar gidanka bata samu hutu ba, baka damu da ko mai daɗi ne ba, ko ba daɗi.

Idan kana da halin da iyalanka za su ci shinkafa da miya da nama, ka ba su shinkafa da mai da yaji, maigida, ka yi laifi, matuƙar ba su suka yi sha’awar cin hakan ba. Idan kana da halin da za ka iya kawar wa iyalinka da kwaɗayi ta hanyar siya masu ɗan abin canza yawu, ka qi siya masu, sai dai kai ka tsaya waje ka ci, ka goge baki, kafin ka shigo gida, maigida, ba ka sauke haƙƙinsu ba.

Idan ka yi tufafi na sanyawa, to fa wajibi ne su ma ka yi masu, wasu malamai suka ce, idan kuɗqqin ɗaya ne gare ka, ma’ana ba ka da wanda za ka yi har ya isa ka yi wa matarka, suka ce ka fara yi mata daga baya ka yi wa kanka.

Kuma bai halasta ba gare ka ya kai maigida ka yi wa matarka ƙeta yayin siya mata kaya, Ina nufin kana da halin siya mata kayan ƙwarai, sai ka siya mata masu arha, kai kuma ka siye mai tsada, idan kana yin haka za ka haɗu da fushin ubangijinka idan ba ka canza ba.

Turare, audugar mata, kayan kwalliya, kuɗin ziyarar iyayenta, tufafi, ci da sha da kuma kula da lafiyarta duk suna kanka maigida sai abin da ta ɗauke ma. Lokuta da dama maza ba su san haƙƙoƙin matansu da ke wuyansu ba, ko kuma sun yi masu bauɗaɗɗiyar fahimta, don haka suke tafiyar da zama da su bisa jahilci. Wannan zai sa duk abinda zuciyarsu ta raya masu shi suke yi a mu’amalarsu da matansu, to ta yaya suke fatan ganin daidai?

Idan har ka yi dogon nazari kan maganganun da suka gabata, ka tabbatar da ka sauke haƙƙin gwargwadon hali, to zan iya cewa, anan ne za mu iya ganin laifin iyalanka akan wannan ɗabi’a da suka ɗauka. Kuma wannan ne zai ba ni damar jan kunne ga matan da suka mayar da wannan hali ɗabi’a bisa ga biyan wata buƙata da sheɗan ya sanar da su ita ce za ta samar masu da biyan buƙata.

Shin uwargida kin san hukuncin sata a Musulunci? Kin san hukuncin zamba cikin aminci a Musulunci? Waɗannan su ne haƙoƙin da ki ka jajubowa kanki yayin da ki ke zura hannu a aljihun mijinki bisa ga son rai. Kuma Ina mai mi ki albishir da cewa, duk abin da ki ka kwasa ba zai ma ki albarka ba, idan burinki ki tara ki zama wata tsiya, to tabbas ba za a kai koina ba sai komai ya watse, idan ba su watse ba a a take kenan ba. Kuma ga nauyin haƙƙin haramun da ki ka kwasa, wanda ba wanda zai iya yafe ma ki sai shi mijin nan naki da ki ka zalunta.

‘Yar’uwa menene makomar ki, a lokacin da mijinki ya mutu ba tare da ya yafe ma ki ɗan-hannu da ki ka yi ma shi ba. Kuma kina da masaniyar da wannan ɗabi’a za ki iya shafawa zuri’arki mumunan gado? Ta yaya?

Ta hanyar shayar da su ɗaya daga cikin ɗabi’un da ake iya gado ta ɓangaren shayarwa ta uwa, wato sata. Masana sun tabbatar da samuwar muradin sata, wanda bature ke kira da ‘shoplift’, idan kuma wannan ya samu ga mutum, duk arzikinsa sai ya yi sata. Sannan yakan yi tasiri ga wasu har ya kai su ga cutar ƙwaƙwalwa mai zaman kanta da ake kira ‘kleptoma’, wato ciyon da ke sa mutum sha’awar yin sata, duk kuma yadda ya yi ba ya iya hana kansa idan yaga abin ɗauka.

Wannan ne ke sa kiga wasu masu arziki a kama su da satar abin da ko kamfanin yin sa suke buƙata suna da abin siya. Don haka nake kira ga mata masu wannan ɗabi’a da su ji tsoron Allah su daina, su san ciwon kansu su nemi sana’a daidai da yanayin su su yi don guje wa sha’awar abinda ba nasu ba tare da kare zuri’arsu daga samun ɗigon abin da suke aikatawa.

Mu tuna, duk wani abu da haramun zata baka, idan ka yi haƙuri, za ka iya samun sa ta hanyar halal.