Sababbin takardun kuɗi: Majalisar dattijai ta nemi CBN ya ɗage wa’adin daina amsar tsofaffin kuɗi

Daga AMINA YUSUF ALI

Majalisar dattijai ta Nijeriya ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun Naira daga 31 ga watan Janairun 2023 da ya sa, ya mayar zuwa 30 ga watan Yunin 2023.

Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata ne, wato a ƙarshen shekarar bara ta 2022 ne dai CBN ya gabatar da sababbin takardun kuɗin da aka sauya fasalin su, wato Naira 1,000, da Naira 500 da kuma Naira 200 da ya yi wa canjin fuska, tare da ba da sanarwar cewa, sababbin takardun za su fara zagawa a hannun al’umma da bankuna daga ranar 15 ga Disambar shekarar baran har ya zuwa 31 ga watan Janairun shekarar bana inda za a haramta amfani da tsofaffin takardun kuɗin.

Shugaba Muhammadu Buhari shi ya ƙaddamar da sababbin takardun kuɗin a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

A kan haka ne, majalisar Dattawan a wani ƙudurin da Sanatan Ali Ndume (APC – Borno ta kudu), ya nemi babban bankin da ya ɗage wa’adin daina amsar tsofaffin takardun Naira watan Yunin 2023.

Ndume, ya bayyana cewa, sam tun daga farko da ma tsarin sauya fasalin kuɗin bai tafi yadda ya kamata ba. Domin a cewar sa har yau zancen da ake yi sababbin kuɗin nan ba su fara Zazzagawa ba a tsakanin al’ummar birni ba balle a yi maganar mutanen karkara.

Ndume ya qara da cewa, yana sane da cewa, tun a ranar Alhamis ɗin 15 ga Disambar 2022 bankuna suka suka bude damar masu ajiyar da su zo su canza kuɗaɗensu zuwa sababbin, kafin nan da 31 ga watan Janairun 2023 da wa’adin tsofaffin kuɗin zai ƙare.

A cewar sa, har yau sababbin kuɗaɗen fa ba su wadata ba, sai ma dogayen layukan da masu ajiyar suke ta jerawa a bankuna don samun sababbin kuɗin. Kuma a cewar sa, gwamnati tana sa ran al’umma za su cigaba da canzar sababbin kuɗaɗen a Bankuna waɗanda za a cigaba da amfani da su a kasuwanci tare da tsofaffin har zuwa 31 ga watan Janairu inda za a haramta amfani da tsofaffin takardun kuɗin gabaɗaya.

Daga ƙarshe, ya bayyana cewa, tabbas al’umma sunabuqatar a yi musu ɗauki a ɗage wannan doka zuwa watan Yunin bana.