MOTHERHEN ta tallafa wa almajirai 50 da rigunan sanyi

Manhaja logo

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

Wata ƙungiya mai tallafa wa mata da ƙananan yara mai suna ‘Motherhen Initiative’ da ke Jos ta tallafa wa wasu yara almajirai su 50 da rigunan sanyi, takalman silifas, garin sabulun wanki da sabulun wanka.

A wani ƙwarya-ƙwaryar taro da ƙungiyar ta gudanar a Unguwar Rikkos da ke garin Jos an faɗakar da almajiran waɗanda shekarun su ba su wuce 5 zuwa 12 ba, da su kasance masu tsaftace jikin su, suna kula da lafiyar jikinsu, musamman a wannan lokaci na hunturu. An kuma tunatar da su kan su nisanci yawace yawace a titi da bin yaran banza, waɗanda za su iya ɓata musu tarbiyya.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Larai Binta Hassan ta bayyana cewa, lura da irin yanayin sanyin da ake yi a Jos, da kuma nazari kan halin da yaran almajirai da marasa gata suke ciki, na yiwuwar takura da kamuwa da wasu cututtuka masu nasaba da lokacin sanyi, ya sa ƙungiyar ta tattara ɗan abin da take da shi, ta sayi suwaitu da sauran kayan da suka raba wa yaran, don su taimaka musu wajen rage tsananin sanyin da ake yi a Jos.

Ta koka da yadda yanzu rayuwa ta koma kowa ‘ya’yansa kawai ya sani, bai damu da halin da yaran da ke rayuwa a titi ko almajirai ke ciki ba. Tausayawa waxannan yaran ne ya sa suka yi tunanin ɓullo da wannan shiri na tallafawa.

Ta buƙaci jama’a masu hali su riƙa tunawa da irin waɗannan yara da sauran masu buƙata ta musamman, a lokaci irin wannan, don a rage musu raɗaɗin da suke fama da shi na rashin samun kulawa da ingantacciyar rayuwa.

A nata bayanin, Hajiya Ladi Sani Mu’azu ta bayyana cewa ƙungiyar su na mayar da hankali ne wajen tallafawa mata mabuƙata da ke buƙatar ɗan ƙaramin jarin yin sana’a, da ilimin ƙananan yara.

Auwal Isa da Audu Shu’aibu daga cikin almajiran da aka tallafawa sun yi farin ciki da taimakon da wannan ƙungiya ta yi musu, tare da alƙawarin kula da tsaftar jikinsu, da mayar da hankali ga karatu. Sannan sun roƙi sauran ƙungiyoyin ba da agaji da masu hannu da shuni, su yi koyi da ƙungiyar Motherhen.