Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa a Kano

Spread the love

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tsare wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Ghadaffi Sagir, bayan da ya yi iƙirarin kashe kishiyar mahaifiyarsa.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna matashin ya aikata ɗanyen aikin ne ta hanyar amfani da makami mai tsini da kuma maƙare ‘yarta.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare da misalin ƙarfe 11:00 a Rijiyar Zaki kusa da Layin Dorawanyan Kifi cikin Ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar.

Da yake tabbatar da cafke matashin a ranar Lahadi, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, ya ce wanda ake zargin ya ce ya kashe marigayiyar ne wai saboda ita ce silar rabuwar mahaifiyarsa da mahaifinsa, Malam Sagir Maimagani.

Shi ma mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar haka.

Ya ƙara da cewa, ‘yan sanda sun fara bincike kan batun.

By Editor