An sako mamallakin tashar AIT, Dokpesi

Daga WAKILINMU

Hukumomi a ƙasar London sun sako mu’assasin kamfanin sadarwar nan na DAAR Communications Plc, wato Cif Raymond Dokpesi, bayan tsare shi da aka yi ranar Lahadi a filin jirgin saman ƙasar.

Da take tabbatar da sakin nasa cikin sanarwar da ta fitar da safiyar Litinin, hukumar kamfanin DAAR ta ce an tsare Dokpesi ɗin ne saboda wani al’amari da ya taso.

“An riƙe Dokpesi na wasu sa’o’i kafin daga bisani jami’an hukumar shige da fice na Birtaniya su buga wa fasfo ɗinsa kan-sarki na shiga ƙasar.

“Cif Dokpesi na godiya dangane da ƙauna da addu’o’in da aka yi masa bayan samun labarin abin da ya faru shi,” in ji sanarwar.