Matar shugaban DSS ta ba da umarnin tsare Abba Gida-gida a Kano,

  • Ta ba da odar kashe hadiminsa

Daga WAKILINMU

Mai ɗakin Shugaban hukumar tsaro na DSS na ƙasa, Aisha Bichi, ta ba da odar a tsare ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Yusuf, tare da hana shi shiga jirgi daga Kano zuwa Abuja a ranar Lahadi da daddare.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito rikicin ya soma ne bayan da tawagar ɗan siyasar ta haifar da cinkoson abubuwan hawan da haifar wa Aisa tsaiko da jinkirin isa inda ya kamata a Babban Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.

Majiyoyi sun ce lamarin bai yi wa Aisha daɗi ba wanda hakan ya sa jami’an tsaron da ke ba ta kariya suka shiga dukan jama’a da motoci wai saboda “rashin girmama Madam”.

Lamarin da ya haifar da hatsaniya a tsakanin jami’an tsron da hadiman dan takarar.

“Al’amari ya yi kamari ne bayan da Aisha ta fada wa Abba ba za su shiga jirgi ɗaya ba kamar yadda aka tsara da farko.

“A nan ta hango daya daga cikin hadiman Abba, Garba Kilo na daukar bidiyonta (da waya),” in ji wata majiya.

Bayanai sun ce an garzaya da Kilo Asibitin Koyarwa na Aminu bayan da ya ci duka bisa umarnin Aisha.

Majiyar ta ce, “Sun yi masa [Kilo] dukan fitar hankali, wanda hakan ya sa Abba cewa atafau jirgi daya za su shiga kamar yadda aka tsara, inda hakan ya kara tinzara ta har da ya kai ga ta ba da umarnin a tsare shi.”

Cikin haka ne aka ce wata tawagar ‘yan sandan sirri ta kange dan takarar Gwamnan har jirgin da Aisha ta shiga ya tashi.

Wani babban jami’in DSS da ya bukaci a sakaya sunansa wanda kuma a gabansa komai ya gudana, ya ce lamarin abu ne da za a iya hana aukuwarsa.

Ya kara da cewa ba daidai ba ne bayyana mai dakin Shugaban DSS din da mafadaciya.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun dan takarar, Sanusi Bature, ya ci tura.

Shi kuwa Kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce, “Babu wanda jami’an suka daka, mukan sa a bi doka kamar yadda tsari ya tanadar.

“Batun cewa an tsare ɗan takarar ba shi da tushe balle ya ja hankalin hukumar ko ma duk wata kafar yada labaran da ta san ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *