Rundunar soji ta yi wa manyan jami’anta sauyin wurin aiki

Daga BASHIR ISAH

A ƙoƙarin da take yi na inganta sha’anin aiki da magance matsalar tsaro, Rundunar Sojin Nijeriya (NA) ta yi wa manyan jami’anta sauyin wajen aiki.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu a ƙarshen mako, ta nuna Shugaban rundunar, Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya amince da sauya wa jami’an wurin aiki.

Su Manjo-Janar da Birgediya-Janar, kwamadoji da sauransu na daga cikin waɗada sauyin ya shafa.

Fitattu daga ciki akwai Manjo-Janar IS Ali daga Hedikwata wanda yanzu shi ne Kwamandan Operation Haɗin Kai da dai sauransu.

Sannan sabbin kwamandojin da aka naɗa sun haɗa da Manjo-Janar CG Musa, Manjo-Janar MS Ahmed, Manjo-Janar BR Sinjen da sauransu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauya wa jami’ai wurin aiki lokaci-lokaci al’ada ce da rundunar ta saba don inganta sha’anin aikin jami’anta.

Sauyin wurin aikin in ji sanarwar zai fara aiki ne daga ranar 11 ga Janairun 2023.