Samar da zaman lafiya haƙƙi ne a kanmu, inji Fasto Buru‎

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Cocin CEIFM da ke yankin Sabon Tasha a Jihar Kaduna, kuma Shugaban Ƙungiyar Samar da Zaman Lafiya da Sasanci ta Ƙasa ‘Peace Revival And Reconciliation Foundation’, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da zaman lafiya a Jihar kaduna da ma ƙasar baki ɗaya.

Yohanna Buru, wanda malamin addinin Kirista ne, ya ce, baya goyon bayan yadda ake musguna wa ’yan jaridu a Nijeirya da kuma yadda malaman addinai suke shiga cikin siyasa, wanda hakan yana da haɗarin gaske. A cewarsa, haƙƙin malamai ne faɗin gaskiya ga ɗaukacin mabiyansu, ba su zama ’yan amshin shata ba.

Fasto Buru, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron liyafar cin abinci domin murnar zagayowar sabuwar shekarar 2023 da ya saba shiryawa duk shekara a Sakatariyar ’Yan Jarida (NUJ) ta Jihar Kaduna.

Fasto ya ce, “’yan jarida na fuskantar cin mutunci, musgunawa da ɗauri a ƙasar nan, duk da irin faɗi-tashin da suke yi wajen ganin an samar da dauwamanmen zaman lafiya a Nijeirya.”

“Musulmi da Kirista duk ’yan adam ne kuma Allah ya halicce mu domin mu zauna tare, saboda haka babu dalilin da zai sanya mu riƙa kashe junanmu, saboda babu addinin da yake koyar da kisa ko tashin hankali,” inji Buru.

A nasa Jawabin, muƙaddashin shugaban ƙungiyar ’yan jarida na Jihar Kaduna, Kwamared Iliya Duniya, ya buƙaci sauran malaman addinai da su yi koyi da Fasto Buru na kawo zaman lafiya da hazin kan al’ummar jihar kaduna baki ɗaya.

Duniya ya ce, lokaci ya yi da za a samar da zaman lafiya a faɗin jihar kaduna musamman yanzu da ake tunkarar zaɓen shekarar 2023. Akan hakan ya buƙaci ɗaukacin ’yan jaridu da ke aiki a jihar kaduna da su riƙa samar da sahihan labarai waɗanda za su kawo haɗin kai da zaman lafiya a faɗin jihar wanda yin hakan yana daga cikin ƙa’dojin aikin jarida.

Taron ya samu halarcin malaman addinai, shugabannin ƙungiyoyi da ’yan jaridu daga kafafen yaɗa labarai daban-daban a faɗin Jihar Kaduna.

By Editor