Dandalin shawara: Cikin da ke jikina ba na mijina ba ne

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Ina yini Asas, ya ayyuka. Don Allah ki ba ni shawara ba tare da kin yi min mummunar fahimta ba. Ciki nake ɗauke da shi, kuma sai aka samu tsautsayi ba na mijina ba ne, duk da cewa bai iya ganewa ba, amma na kasa samun natsuwa akan sirrin da na voye. Watanin baya na yi tafiya ganin gida garimu……, to kafin na tafi, maigidana ya yi fama da zazzaɓi, don haka mun kwana kusan goma sha bai taɓa ni ba, da ya samu sauƙi kuma sai na fara jinin al’ada, a cikin wannnan halin na je garinmu.

To fa nan na haɗu da wani tsohon saurayina, daga nan sheɗan ya shiga bayan na gama al’ada. To bayan na dawo gida na ɗan fara laulayi, na gane hakan don ba cikina na farko ba ne, to ban dai sanar da mijina ba, sai dai da abin ya yi yawa ne na je asibiti, inda aka tabbatar min Ina ɗauke da juna biyu na wata ɗaya daidai, wanda idan aka yi lissafi zai kama bayan kammala al’adata a garinmu kenan, kuma shine adadin kwanaki 50 mijina bai kusance ni ba.

to sai na yi gum da bakina, sai dai da na dawo a daren na tabbatar maigidana ya kusance ni, kuma tun ranar sai da muka kwashe kwanaki bana bari ya yi fashi, da haka na kawar da duk wani abu da zai sa shi yin lissafi, sannan bayan wata guda na gaya ma shi Ina da ciki. Bai kawo komai ba ko don na ce masa cikin wata ɗaya ne. don Allah ki ba ni shawarar yadda zan yi don na kasa samun nutsuwa, kuma Ina tsoron in sanar da mijina ya rabu da ni don Ina son sa.

AMSA:

Lafiya ƙalau, alhamdu lillah. Kafin mu kai ga ba ki shawara ‘yar’uwa, bari mu ɗan yi waiwaye zuwa ga bayanai da suka gabata a addinin Musulunci kan irin wannan matsala idan ta taso. Littafi mai tsarki ya sanar da cewa, amfanin aure shine, rufe ido daga haramun ta ɓangaren sha’awa kenan, don haka, kin yi aure ne don ki kauce wa zina.

Sai kuma aka ce, idan ba ku samu mazan da za su aure ku, ko mazan da ba su samu abin aure ba, su yi azumi, don ya hane su daga zina. Aka ƙara da cewa, su maza na da dama akan abin da hannunsu na dama ya mallaka na daga bayi, kuma za su iya auren baiwa idan matsi ya yi matsi, sai dai hukuncin da ke tattare da auren baiwa ya sa aka so a yi haƙurin idan za a iya.

Wata ayar dake bayani kan mutanen kirki ta ce, su ne waɗanda ke kiyaye farjinsu, har sai ga matayensu ko abinda damansu ta mallaka.” Daga ƙarshe ayar ta ce, baya ga waɗannan hanyoyi da aka bayyana duk wanda ke bin wata hanyar don saduwa da wata mace da ta fita daga cikin biyun nan da aka lissafo, to fa ya shiga layin waɗanda Al’ƙur’ani mai tsarki ya kira da ‘yan ta’adda masu aikata kaba’irai.

Haka kuma ya bayyana mana hukuncin mace ko namijin da suka aikata zina. Idan ba su da aure, za a yi masu bulala 100, idan kuwa masu aure ne, za a jefe su har su mutu. Amma da sharaɗin sai an kama su turmi da taɓarya.

Me ya sa na kawo wannan dogon bayani? Saboda ki fara fahimtar hukuncin abinda ki ka aikata a Musulunce, ki fahimci ko akwai rangwame da addini ya yi ga masu zina ko ba su uzuri, kafin mu kai ga irin furucin da Asas zata yi kan lamarin.

Idan har kina tunanin zan ma ki uzuri ko in sanar da ke tsautsayi ne ko ba ki da laifi, Ina mai ba ki haƙuri, domin ba za ki ji wannan daga bakina ba, saboda babu uzuri akan abinda ki ka aikata. Idan har kina buƙatar mijinki kafin ki tafi, ai za ki iya jiran ki yi tsarki, idan kin samu natsuwa, sai ki yi tafiyar, idan kuma tafiyar ta zama dole a wannan lokacin, za ki iya yin azumi don sauƙaƙa wutar sha’awa, baya ga haka, babu dalilin da zai sa ki sakar wa wanda ya yi son ki a baya fuska a matsayinki ta matar aure, har ta kai kin ziyarce shi ko ya ziyarce ki, har shaiɗan ya samu dama irin wannan.