Kotu ta ɗaure masu taimaka wa ‘yan bindiga a Neja

Daga BASHIR ISAH

Wata Koton Majastare mai zamanta a Minna, babban birnin Jihar Neja, ta ɗaure wasu mutum uku shekara uku a gidan yari bayan da ta same su da laifin taimaka wa ‘yan bindiga a jihar.

Alƙalin kotun, Hajiya Fati Kabir, ta ce masu laifin za su yi zaman kurkukun ne haɗi da aiki mai wahala.

Kotun ta kama Abubakar Abdullahi da Abubakar Musa da kuma Kabir Mohammed ne da laifuka biyu, wato taimaka wa ‘yan ta’adda da taimaka wa masu laifi wajen tserewa.

Laifukan da Kotun ta ce sun saɓa wa sassa na 3 (1) da na 4 (1) na dokar Jihar Neja ta 2016 kan haramta garkuwa da satar shanu.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Thomas Irimiya Peter ASP, ya shaida wa kotun cewa, a ranar 14 ga Afrilun 2022 ne ‘yan sandan yankin Mashegu suka cafke masu laifin ɗauke da ƙwayoyi inda suka fake da cewa su likitoci ne.

Ya ƙara da cewa, an samu nasarar kama su ne sakamakon muhimman bayanan da suka samu.