Mabiya Shi’a sun gudanar da taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba

Daga MOHAMMED ALBARNO

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba, Mabiya Shi’a ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Zakzaky suka yi taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba wanda suke zargin sojojin Nijeriya da barin wuta kan ’yan uwansu a shekara ta 2015.

Ranar 12 Disamba, rana ce da dukkan wani mabiyi na Sheikh Zakzaky ke ɗaukarsa a matsayin rana ta baƙin ciki. Rana ce da sojoji ke zargin ’yan shi’a da tare wa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na lokacin, Laftanar-Janar Tukur Burutai, hanya.

Shekaru 7 baya, a shekara ta 2015, anyi varin wuta a Zaria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. A rahoton ɓangaren sojin Nijeriya sun bayyana cewa sama da mutane 350 ne suka mutu tare da binne su a kabari ɗaya, yayin da su kuma ɓangaren ’yan shi’a na cewa sama da mutane dubu ne ba a gani ba. Yayin da dama aka jikita su da harsashai masu rai.

Daga cikin waɗanda suka samu raunin harbin harsashi akwai shugaban nasu na ’yan uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim Zakzaky, tare da matarsa Malama Zeenah. Yayin da wasu daga cikin ‘ya’yansu na cikin mutane dubu da ake zargin an kashe su a shekara ta 2015 bayan wasu 3 da aka kashe su a shekara ta 2014 lokacin Jonathan ke karagar mulkin ƙasar.

Matar Sheikh Zakzaky, mahaifiya ga ‘ya’ya 6 da aka kashe, ita ce babbar baƙuwa a wajen taron tunawa da wannan ranar. Taron wanda ya gudana a baban Birnin Tarayya Abuja.

Malama Zeenah, ta isa filin taro, yayin da wuri ya ɗauki kuwa, da jinjina gare ta, wasu ma ba su iya zuwa wajen ba, saboda kada su ga hali da ta ke ciki, yayin da tafiya ma da ƙyar ta ke iya yi.

Daga cikin jawaban nata, ta bayyana mahutuntar Nijeriya a matsayin waɗanda suke so su kawar da Harkar Islamiyya saboda tonan asiri da harkar ke yi na irin zalunci da mahukunta ke yi.

Malama Zina, ta bayyana cewa, duk abin da mahukunta za su yi, harkar za ta cigaba da motsawa.

Ta ce, “mahukunta suna yin abun ne saboda duniya ne, kuma a nan duniya, yayin da mu kuma muna yi duniya da lahira”.

Ta ƙara da cewa, koda za su shirya harsashi harshai, su ƙara da bom, wannan ba zai razana su ba.

Har ila yau, Malama Zina ta ce, ai sun aiwatar da abinda suka son aiwatarwa na kisa, sun sa mota sun take mutane, ciki harda yara da mata.

Bayan ta kammala jawabanta, Malama Zeena ɗin ta fito cikin yanayi, ta hau mota ta koma gida. Yayin da taron ya ci gaba da gudana, tare da sauraran jawabi na kai tsaye daga ɗakin jagora na ’an uwan Musulmai, Sheikh Zakzaky.

Daga cikin jawaban na ahugaban na su, ya fara jawabinsa ne tare da yiwa masu sauraro jajen abinda ya faru a wannan watar.

Daga cikin kwanaki 3 da za su yi na gudanar da wannan taron, 12, 13, 14, sun yi daidai da lokacin tunawa da shahadar Sayyada Fatima Azzahara ɗiyar Manzon Allah (SAWW).

Jagoran na ’yan Shi’a, ya yi jawabi kan irin yadda mahukunta suka yi ƙeta na ƙona mutane tare kisa, ya ce, ba zai ya riƙa maimaita wa ba, wanda idan mutum yana buƙata sanin abubuwa game da wannan, zai iya bibiyar hiraraki da aka yi da mutane kafin wannan lokaci.

Sheikh ya bayyana cewa, wannan kisa da aka yi musu a 12 12 2015, ƙaraƙashin mulkin Janar Buhari, ya goge duk wani abu da aka musu, wanda hakan ya ciki kundun tarihi nasu da ba za su taɓa mantawa ba.

Daga ƙarshe dai aka rufe taro da addu’a, an kuma tashi lafiya, ba tare da wani abu ya faru ba.