‘Yan Arewa na sayar da katin zaɓen su Naira 2,000, inji NEF

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta yi zargin cewa ‘yan Nijeriya mazauna arewacin ƙasar na sayar da Katin Zaɓen d’Dindindin (PVCs) kan Naira 2000.

Daraktan Yaɗa Labarai na NEF, Hakeem Baba Ahmed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, NEF ta tabbatar da abin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce game da lamarin.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne INEC ta bayyana cewa ta bankaɗo yadda wasu ’yan Nijeriya ke sayen katin zaɓe na PVC tare da gargaɗin cewa za a ɗaure masu aikata wannan laifi a gidan yari.

Sanarwar ta NEF ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa ta’adar ta yaɗu sosai kuma ana zuwa wajen raunanan mutane ne a wurare da dama na Arewa da wasu sassan ƙasar domin a yaudare su a saye katin zaɓen su.

Ta ce, ƙungiyar ta bi diddigi kan wannan lamari mai cike da damuwa, inda ta shawarci shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki kan illolin da ke tattare da tauye wa ɗumbin ’yan kasa ’yancinsu.

“NEF ta yi kira ga INEC da ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a game da wannan mummunar barazana ga ’yancin masu kaɗa ƙuri’a.

“NEF ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su ƙara zage damtse wajen yaƙi da munanan barazanar da ka iya hana miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a a Arewa, da sauran ’yan ƙasa da dama a wasu sassan ƙasar nan kaɗa ƙuri’a.