DSS ta janye jami’anta daga tawagar Gwamna kan rashin jituwa da ‘yan sanda

Daga WAKILINMU

Hukumar tsaro ta DSS ta janye jami’anta daga tawagar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke.

Mamhaja ta kalato cewa, hamayyar da ke tsakanin jami’an DSS ɗin da na ‘yan sandan yankin ce ta haifar da janye jami’anta da DSS ta yi.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar, a makon da ya gabata babban ofishin DSS ya janye jami’ansa daga tawagar Gwamna Adeleke, tare da buƙatar gwamnan ya kiyaye tsarin ba da tsaro yadda ya kamata.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Mai magana da yawun Gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin fahimtar da ya shiga tsakanin jami’an DSS da na ‘yan sandan da ke ƙarƙarshin Gwamnan.

Binciken Manhaja ya gano cewa, babban ofishin DSS bai ji daɗin abin da aka yi wa jami’ansa ba shi ya sa ya ɗauki matakin janye jami’an nasa.

An ce Dogarin Gwaman (ADC) ne ya shigo da jami’an ‘yan sanda tare da ɗora su a kan aikin da na jami’an DSS ne.