Da Ɗumi-ɗumi: Argentina ta lashe Kofin Duniya

A ranar Lahadi aka buga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a ƙasar Qatar.

An buga wasan ƙarshen ne tsakanin Argentina da Faransa.

Bayan fafatawa na tsawon minti sama da 100 a wasan, a ƙarshe Argentina ta yi nasara a kan Faransa, inda ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yanzu dai ya tabbata Argentina ce ta zama gwarzuwa a gasar wannan karon.

Cikakken bayani na nan tafe…