Pierre Moussa: Hanyar da Ƙasar Sin ke bi ta zamanantar da ƙasa abun koyi ne ga ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA

Shugaban jam’iyyar PCT mai mulki a kasar Congo Mr. Pierre Moussa, ya ce hanyar da kasar Sin ke bi wajen zamanantar da kasa, abun koyi ne ga kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afirka.

Moussa ya bayyana hakan ne, yayin wata zantawa da ya yi kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya yi tsokaci game da jigon “samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire” da sauran su, yana mai cewa, hakan zai wayar da kan kasashen duniya masu yawa, musamman wadanda suke a nahiyar Afirka.

Jami’in ya kara da cewa, manufofin bunkasa kasa na Sin, abun koyi ne ga kasashen dake son zabar tafarkin ci gaba mai inganci, wanda hakan zai iya ba su damar tunkarar kalubalen yau da na gobe.

Moussa mai shekaru 81 a duniya, ya sha ziyartar kasar Sin, kuma a tattaunawar tasa ta kwanan baya, ya yi fatan ganin JKS ta ci gaba da karfafa kawance, da hadin gwiwa da jam’iyyar sa ta PCT, wanda hakan zai ingiza cikakkiyar hadin gwiwa daga dukkanin fannoni, tsakanin Sin da Jamhuriyar Congo, ta yadda hakan zai amfani al’ummar kasar.

Mai fassara: Saminu Alhassan