Matsalar ƙarancin likitoci na ƙara taɓarɓarewa a Nijeriya, inji NARD

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Nijeriya (NARD) ta ce, ƙarancin likitocin da ake fuskanta a ƙasar ya yi munin da a yanzu likita zaya ne ke duba marasa lafiya 10,000.

Ƙungiyar ta ce, a halin da ake ciki, likitocin da ake da su a faɗin ƙasar ba su wuce 10,000 ba.

Ta ce, adadin likitocin raguwa ya ke kullum sakamakon barin ƙasar da suke yi zuwa aiki a ƙasashen waje.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dokta Emeka Orji, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai.

A cewarsa, kimanin likitoci 100 ne ke barin ƙasar zuwa ƙetare duk wata don neman aiki.

Ya ce, daga cikin likitoci 80,000 da suka yi rajista, kimanin kaso 64 cikin 100 ba sa aiki saboda wasunsu sun yi murabus, wasu sun bar ƙasar, wasu sun sake aiki, wasu kuma sun mutu.

Shugaban ya kuma ce kafin wannan lokacin, “Likitoci 16,000 ake da su, amma yanzu ba su wuce dubu tara zuwa 10 ba.”

Hakan na nufin likitocin da ake da su da za su kula da al’ummar Nijeriya su sama da miliyan 200, ba su wuce guda 10,000 ba.