Sana’a wata hanya ce ta samar wa kai ‘yanci – Kadeeja Ahmad

“Ki yi sana’ar da zuciyarki ke so, ba wadda ki ka ga wani ya yi ba”

Daga AISHA ASAS

(Ci gaba daga makon jiya)

A satin da ya gabata, idan mai karatu bai yi rashin mallakar jarida mai farin jini Manhaja, ba, mun ɗauko fira da matashiya Kadeeja Ahmad, wadda ta kasance jajirtacciya a vangaren neman na kai, ta hanyar zama ƙwararriyar mai ƙera takalma kuma ta yi shiri tsaf wurin ganin duk wani qalubale da zai tunkaro ta bai tsorata ta ko ya sare mata gwiwa ba, har ta kai a yanzu ta ke kwankwaɗar romon haƙuri da kuma tarairiyyar sana’arta da ta yi. A farkon tattaunawar Kaddeja wadda ke da kamfanin takalman KAD Shoes ta bayyana mana tarihi da kuma nauyin karatun da ta samu, har ta gangara da mu lokacin da ta fara sana’a da adadin kuɗin da ta fara da su zuwa ‘yan matsalolin da ta dinga yin tuntuve da su. Mun tsaya a daidai tambayar me ya sa ta zavi yin sana’a a lokacin da ta ke karatu, inda kafin ta kai ga amsar ne muka ja birki, don haka, idan kun shirya, ga ci gaban tattaunawar:

MANHAJA: Me ya sa ki ka zaɓi yin sana’a a lokacin da ki ke karatu, kasancewar da yawa suna kallon boko karan kansa a matsayin hanyar samun abin na kai?

KADEEJA: Wannan ba zai rasa nasaba da yadda na taso da shauƙin yin sana’a, tun Ina ƙarama nake sana’a, a lokacin da ma shekarun ba su kai na sanin muhimmancin sana’ar ko su kansu kuɗin ba, kawai dai in miƙa, a bani kuɗi, na sayar da abinda nake saidawa, sai in ta murna. Baya ga haka, yana ɗaya daga cikin manyan buruka da nake da su, zama hamshaƙiyar ‘yar kasuwa.

Waɗanne irin qalubale ki ka fuskata a wannan sana’a?

Dama ita kanta rayuwa gabaɗayan ta kewaye ta ke da ƙalubalai, don haka bazan ce ban fuskanci ƙalubale ba, sai dai da yawansu sun samu ne a farkon farawa, kafin mu yi ƙarfi. Daga ciki akwai rashin samun kayan aiki irin wanda ya dace da takalman da ake buƙata, kamar yadda na faɗa a baya, wannan matsala kan iya haifar da rashin fitar takalman yadda ake so, sai kuma ta ɓangaren masu sa ayi masu da yawa, za ki ga wasu na bada takalma kala daban-daban kuma da yawa ayi masu kowanne ɗaya-ɗaya ko biyu, to ta sanadiyyar ba iri ɗaya ne ba dukka wani lokacin akan samu tsaiko wurin kammalawa har mai kaya ya zo karɓa ba a kammala ba, saboda ba ɗai yake da wanda za ka yi wa yanka iri ɗaya ba, amma a yanzu kam mun gano gadar zaren, duk da ba mu kawo karshen ta ba, sai kuma matsalar da ta samu a farkon farawa, wasu za su zo, suga takalma, su yaba, kuma su nemi a ajiye masu, za su dawo, su kawo kuɗi, su karɓa, amma sai ka yi ta ajiya ba su dawo ba, Ina magana ne a farkon fara sana’ar.

Su waɗannan takalma da ku ke yi, shin kun tsaya ne iya yi wa masu buqata ne ko kuwa ku kan yi ku ajiye ga masu zuwa su duba su saya?

Sha’anin takalma yana da ɗan wuyar sha’ani don haka ba mu cika yi masu wani yawa mu ajiye ba, harkar ta kasu kashi biyu ne, wasu za su iya zuwa, su kawo irin takalman da suke so ayi masu tare da adanin kowanne, to, a wannan ɓangare zavi biyu ne, wasu za su iya neman ayi masu waɗanda ingancinsu bai kai irin waɗanda na saba yi ba, to anan ba zan sa sunan takalmana ba, saboda zai ɓata min kasuwa, sai dai in yi ma marar suna ko wani sunan da ka buƙaci a sa a maimakon nawa ɗin. Ko kuma in yi mai inganci irin yadda nasaba yi,

kuma in saka ma sunan nawa, sai dai zan baka ne a matsayin sari, tunda da yawa ka ke so. Ko kuma masu kawo takalma masu tsada da kamfanin da ya yi su sananne ne duk a duniya, sai su nemi a saka musu sunan kamfanin.

Waɗanne nasarori aka samu ta ɓangaren cigaba a ƙwarewa?

Akwai cigaba sosai ta wannan ɓangare, idan aka duba yadda a yanzu ba takalman da ke tsorata ni, duk wani takalman da a baya bazan iya yinsu ba yanzu zan iya. Dama kuma babban burina na dinga yin takalman da ake yi a qasashen da suka yi shuhura a yin takalma, in samar da kwatankwacin ingancin su, amma cikin sauƙin kuɗi, ma’ana yadda ba zai kai tsadar nasu ba.

To bari na ɗan mayar da ke baya kaɗan. Kinyi maganar matsala da ake samu na samun wasu daga cikin kayan yin waɗansu takalma. Shin kina da wani shiri ko kuma buri na ganin cewa, kin fara siyo waɗannan kayan aikin daga ƙasashen da ake samun su?

Tabbas Ina da wannan burin na siyo kayayakin aiki daga waje, don samun damar yin takalman ɗari bisa ɗari.

Kina ganin idan aka samu cikar wannan burin takalman za su iya yin sauqi kamar yadda ki ke fatan su yi?

Sosai kuwa, ai idan ki ka yi duba da cewa, a nan za a yi takalman, don haka akwai kuɗaɗe da dama da za a tsallake da ake samu idan za a shigo da takalman daga wajen.

Mu koma ɓangaren iyali. Kina da aure?

(Dariya) ba ni da aure, ban taɓa yi ba.

Akwai wasu da ke ganin idan mace ta fara da sana’a ko aiki kafin aure, kuma har ta yi ɗan nisa, ma’ana ta samu abin kanta, takan samu matsala wurin zaɓen mijin aure, ta yadda zamani ya lalace, mazan ma sun bi layin mata wurin kwaɗayin abin hannun abokan zaman aurensu. Wannan ke sa maza da yawa za su zo neman auren ne don matsin da suka ango a wurin macen. Shin ke a wurinki akwai wannan tunanin a rainki?

(Dariya) to bazan ce ba wannan tunanin a tare da ni ba, sai dai tunanin sai ka gwada mazan ne auren zai kasance na kawar da wannan tunanin daga raina, ma’ana a zaman da za ku yi ne za ki iya gano inda ya dosa, kuma ni ba kowa ma nake amincewa da shi ba.

Kenan kina da tabbacin hakan ba zata kasance a ɓangarenki ba, saboda kin yi wa hakan tanadi, ma’ana za ki iya gane manufar da ya zo da ita?

Tabbas zan iya gane wa, asalima bazan kula ma wanda nasan na fi ba.

Sai mai kuɗi sosai kenan?

(Dariya sosai). A’a ba lallai sai mai kuɗi ba, ai duk mutumin da ka ɗan zauna da shi za ka iya fahimtar ka fi shi ko ya fi ka, irin dai yadda ba zai kasance yana kallon na hannunki ba.

To amma ai wani lokacin akan samu su kansu masu abin hannun nasu suna son su samu mata masu abin hannunsu.

Eh to, wannan bai dame ni ba, saboda kaima kana da naka don haka ba sa wa nawa ido za ka yi ba, ni a gani na ba shi da matsala idan iya nan ya tsaya, koda kuwa hakan na nufin ni zan kula da kaina, kaima ka kula da kanka. Kinsan a wannan zamani da muke ciki, maza da yawa basa son auren macen da za ta zame masu kaya, a ce komai sai miji ya yi ma ki, ba ki iya tsinanawa kanki komai.

Mu ji ta ɓangaren abinci. Wane irin abinci ki ka fi so?

Dambu.

Ta ɓanagaren kayan kwalliya fa?

Gaskiya kwalliya bata dame ni sosai ba, in ba dai zan ɗauki hoto ba.

Kayan sawa wane ne zaɓinki?

Gaskiya ba ni da inda na fi raja’a a kayan sawa, kawai dai Ina son duk wanda ya yi min.

Daga ƙarshe, wane irin kira ki ke da shi ga matan da ke zaman kashe wando?

Shawarar dazan ba su ita ce, su ta shi su nemi na kansu, kuma yayin zaɓin abin yi, su zavi abinda suke son su yi har a cikin ransu, ba wai abinda suka ga wani ya yi ba, saboda abinda ka ke so, kuma zuciyarka ta aminta da shi zai taimaka ma matuƙa wurin kwankwaɗe duk wani ƙalubale da zai yi wa sana’ar wanka, za ka ɗaura aniyyar duk wuya, duk runtsi ba za ka bari matsalolin ta su sare ma gwiwa ba har sai ka kai ga garin cikar burinka. Kuma sana’a a wannan zamani da muke ciki wata hanya ce ta samar wa kai ‘yanci, domin mace mai sana’a ta bambanta da marar yi ko ga yanayin yadda duniya ta ke kallonta.

Mun gode.

Yawwa, ni ma na gode.