Dandalin shawara: cikin da ke jikina ba na mijina ba ne

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Ina yini Asas, ya ayyuka. Don Allah ki ba ni shawara ba tare da kin yi min mummunar fahimta ba. Ciki nake ɗauke da shi, kuma sai aka samu tsautsayi ba na mijina ba ne, duk da cewa bai iya ganewa ba, amma na kasa samun natsuwa akan sirrin da na ɓoye.

Watanin baya na yi tafiya ganin gida garimu……, to kafin na tafi, maigidana ya yi fama da zazzavi, don haka mun kwana kusan goma sha bai tava ni ba, da ya samu sauqi kuma sai na fara jinin al’ada, a cikin wannnan halin na je garinmu.

To fa nan na haɗu da wani tsohon saurayina, daga nan sheɗan ya shiga bayan na gama al’ada. To bayan na dawo gida na ɗan fara laulayi, na gane hakan don ba cikina na farko ba ne, to ban dai sanar da mijina ba, sai dai da abin ya yi yawa ne na je asibiti, inda aka tabbatar min Ina ɗauke da juna biyu na wata ɗaya daidai, wanda idan aka yi lissafi zai kama bayan kammala al’adata a garinmu kenan, kuma shine adadin kwanaki 50 mijina bai kusance ni ba.

to sai na yi gum da bakina, sai dai da na dawo a daren na tabbatar maigidana ya kusance ni, kuma tun ranar sai da muka kwashe kwanaki bana bari ya yi fashi, da haka na kawar da duk wani abu da zai sa shi yin lissafi, sannan bayan wata guda na gaya ma shi Ina da ciki.

Bai kawo komai ba ko don na ce masa cikin wata ɗaya ne. don Allah ki ba ni shawarar yadda zan yi don na kasa samun nutsuwa, kuma Ina tsoron in sanar da mijina ya rabu da ni don Ina son sa.

AMSA:

Idan za mu yi wa abinda ki ka aikata suna ba zai taɓa zama a rukunin kuskure ba, sai dai ba hukunci mu ke da ƙudurin bayyana wa ba. Wannan laifin da ki ka aikata tsakanin ki ne da mahaliccin ki, idan ya ga dama ya yafe ma ki, idan kin nemi gafarar Sa. Sai dai abinda yake maƙasudin wannan rubutu shine mafita da ki ka nema.

Idan har zuciyarki ta kasa natsuwa kan wannan ɗanyen aikin da ki ka aikata, to alamu ne na da sauran imani a tare da ke, domin wanda ya bushe fitilarsa ba abinda zai ji don ya kai shege gidan aure. Don haka yake da kyau ki aikata abinda ya dace kada ki biye wa son rai.

Ki sa mijinki a matsayin da ki ke a yanzu, ma’ana idan da za a ce a waye gari kina da ciki, ki ka zo haihuwa, sai a ce mijinki ya yi wa wata ciki, lokacin da ki ka haihu sai a yi ma ki musanya da wannan ɗan na shege, a gabatar mi ki da shi a matsayin ɗan da ke ki ka haifa, ki shayar da shi, ki kula da shi, kashi, fitsari har zuwa barcinsa, shin ya za ki ji a lokacin da ki ka samu labari bayan kin gama wahala da shi?

Shin ba za ki so a ce tun a farko mijin ya sanar da ke gaskiya ba, ko da kuwa za ki ƙi zama da shi idan ki ka san gaskiyar? Wane zai fi ma ki zafi, sani tun ba ki karɓi yaron ba da bayan kin gama wahala da shi?

Ki yi wa mijinki adalci ta hanyar yin abinda ki ka san za ki so ayi miki idan shi ne ya aikata abinda ki ka yi.

A ɓangaren tsoron rabuwa da ki ka kawo ba zai zama hujjar da zai sa ki rufe mijinki kan wannan lamari ba. Matsalar biye wa zugar sheɗan kenan, abinda za ka aikata kawai zai sanar da kai ba tare da samar ma ka mafita akan abinda zai biyo bayan ɗanyen aikin da ya tura ka aikatawa.

Na sani a yanzu ba za a rasa sautin muryar sheɗan da yake sanar da ke zubar da cikin ne mafita, sai dai Ina mai tabbatar miki ita ma wannan gadar zare ce ya shimfiɗa miki, ba za ki gane ba sai bayan kin aikata. Laifi biyu da biyu.

Kin yi zina da aurenki kuma kin yi kisan kai ta hanyar zubar da cikin. Shin me za ki gaya wa ubangiji a gobe Ƙiyama, ko idan an yi daidai da tsautsayi ki ka gangara me ki ke tunanin zai zama makomar ki?

Don haka idan har kin yi nadamar abinda ki ka aikata, to fa hanya ɗaya ce, ki tubar wa Allah, ki nemi gafarar Sa, sannan kuma ki sanar da mijinki gaskiya, ta hakan ce kawai za ki iya samun damar neman gafara daga wurin sa. Kuma wataƙila idan Allah yaga niyyarki zai iya kawo abin da sauƙi.

Na san wasu za su iya kawo miki hukuncin da aka ce macen da ta yi zina sau ɗaya zata iya tuba, ta nemi yafiyar Allah, ta kuma yi gum da bakinta, ba tare da ta sanar da mijinta ba, a ƙoƙarin Musulunci na hana yawaitar saki, sai dai fa wannan hukuncin na kan matan da suka yi zina kawai, ba tare da yin guzuri irin naki ba.

Abu na ƙarshe, ki tuna zamani ya zo da cigaba ta ɓangaren samun sauƙi wurin gane jini, ma’ana sanin ƴaƴan da suke naka, shin ba kya tunanin agaba wani abu zai iya tasowa ya gane ba ɗansa ba ne?

Za ki iya rayuwa da fargabar ranar da zai san ba ɗansa ba ne? Me zai iya faruwa idan ya gane bayan ya gama hidimta wa abinda aka haifa? Ki yi nazari kan waɗannan kafin ki yanke hukuncin ɓoye masa. Ki tuna, masu iya magana suna cewa, ramen ƙarya, ƙurare ne.