2023: Gobe Matawalle zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe

Daga MUHAMMAD SANUSI, Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle zai ƙaddamar da yaƙin neman zaben gwamna a karo na biyu a ranar Talata.

Jawabin haka ya fito ne ta bakin Daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Gwamna Bello Matawalle a shekarar 2023, Alh. Ibrahim Ɗanmalikin Gidan Goga a wani taron manema labarai aka shirya a Gusau, babban birnin jihar.

A cewarsa, an shirya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a garin Ƙaura Namoda hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda ta jihar.

Ya ƙara da cewa, majalisar kamfen ɗin Gwamna Bello Matawalle ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ta kammala duk wani shiri na yaƙin neman zaɓen da ya dace don ziyartar dukkanin ƙananan hukumomi 14 da jihar ke da su.

“Tuni hukumar yaƙin neman zaɓen tana aiki tukuru domin ganin ba a samu cikas ba.’,” in ji shi.

Haka nan, ya jaddada cewa Jam’iyyar APC za ta lashe dukkan muƙaman siyasa a jihar a yayin zaɓe mai zuwa, yana mai cewa majalisar kamfen ɗin za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an gudanar da yaƙin neman zaɓen na APC a jihar cikin lumana.

Ɗanmalikin Gidan Goga ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar APC da magoya bayanta da su kasance masu bin doka da oda musamman a lokutan yaƙin neman zaɓe da kuma lokacin zaɓe mai zuwa domin samun nasarar APC a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.