Kudancin Nijeriya ya ba wa Arewa tazarar shekaru 40 a fuskar arziki – Bankin Duniya

AMINA YUSUF ALI

Bankin Duniya ya bayyana cewa, jihohin Arewacin Nijeriya sai sun ɗauki tsahon shekaru 40 kafin su kamo jihohin Kudu a fannin tattalin arziki duba da yanayin yadda abubuwa suke tafiya a halin yanzu.

Bankin ya bayyana cewa, yanayin rashin cigaba da bunƙasa da yankin Arewa yake yi na tsahon lokaci shi ya jawo wannan wawakekiyar tazara a tsakanin yankunan guda biyu.

A cewar Bankin an bar yankin Arewa a baya a fannoni kamar noman zamani, harkar ma’adanai da masana’antu.

Wannan ra’ayi yana ƙunshe ne a wani jawabi a kan tattalin arzikin Nijeriya (CEM) wanda bankin ya saki a ranar 15 ga Disamba a Abuja. A wani taro na wanda mutane daban-daban a faɗin Duniya suka halarta ta intanet.

Kundin mai shafi 72 ya yi bayani ne a kan hanyoyin samar da cigaba da kuma samar da aikin yi. Wanda ya shafi binciken da aka gudanar a shekarar 2000 zuwa 2021.

Haka kuma ya jero jiga-jigan ƙalubale da kuma damarmakin da za su sa a samu bunƙasa da cigaba da sauri tare da samar da abin yi a Nijeriya ma bakiɗaya.

Rahoton ya bayyana zurfin tazarar yankin Arewa da Kudu ta fuskar tattalin arziki da cewa, tsananin talaucin ya kai ninki 20 a jihar Sokoto wanda ita ce jiha mafi talauci wanda ya kai kaso 87.7 idan ka kwatanta shi da jihar Legas wanda yake da kimar talauci ta kai kaso 4.5 wato daga sakamakon binciken da aka yi a 2018/2019.

Hakazalika, a cewar rahoton, ita kanta ƙasar Nijeriya a yanayin da ake ciki za ta iya kai wa yanayin tattalin arzikin da take a baya. Wato dai tun daga karayar tattalin arzikin da ƙasar ta shiga a shekarar 2016.

A cewar Bankin, duk da albarkatun qasa masu tarin yawa da ƙasar take da su, da yawan al’umma matasa majiya qarfi, Nijeriya a tsaye take cak a fannin arziki a tsahon shekaru 100 kuma har yanzu ta kasa kamo sauran ƙasashen tsararrakinta domin tana watsi da masu zuba jari na ƙasar waje kuma cinkoson al’umma yana tilasta wa matasanta barin ƙasashen ƙetare domin samun guraben aiki a can.

Hakazalika a cewar sa, duk da tashin da farashin fetur ke yi ba ya ƙara ƙarfin tattalin arzikin ƙasa ko bunƙasa damarmakin samun aiki.

Shawarar da ta kamaci Nijeriya dai a cewar rahoton CEM shi ne, ƙasar ta mai da hankali wajen inganta kasuwanci kuma ta samar da yanayin kasuwanci mai kyau. Sannan kuma a inganta tsarin canjin kuɗi kuma a cire shamakin kasuwanci tsakanin ƙasashe, a rage dogaro da man fetur, da magance matsin tattalin arziki wanda aka ce ya jefa ‘yan Nijeriya miliyan 8 a cikin ƙangin talauci a cewar wani bincike da aka yi tsakanin shekarar 2020 da 2021.

In dai an kiyaye wannan a cewar sa, Nijeriya za ta iya zama tauraruwa mai haskawa a Duniya ta fuskar tattalin arziki.