Okupe ya yada ƙwallon mangoro a Leba

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Siyasar zaɓen 2023 na ƙara kankama inda ’yan takara da muqarrabansu, ke bayyana manufofi da abubuwan da su kan yi alƙawarin za su aiwatar in an ba su dama. Akasari a kan ce alƙawarin ’yan siyasa tamkar zane ne kan ruwa don a kan ambata komai cewa za a gyara kama daga ilmi, tsaro, tattalin arziki, noma, kiwo, zamantakewa da sauran su amma ba lalle ne ka ga duk waɗanda su ka ɗauki alqawuran sun cika kashi 20% ba. Hasalima wasu kan maida gwamnatin tamkar ta ’yan uwa ne da abokai a yi ta sharholiya a tsarin a ci duniya da tsinke.

Wannan dalili ya sa wasu daga masu kada ƙuri’a su ka ɗauki alwashin sai lalle sun fahimci gaskiyar ’yan takarar kuma ko da hakan zai kai ga a rubuta takardar yarjejeniya a rantaba hannu. Wasu kuma sun ga gara fa a yi siyasar kwai a baka ya fi kaza a akurki a ɗan miqa mu su kason su kafin zaɓe sai su mara baya in ya so daga bisani duk abun da ya faru ba kare bin damo. Kazalika ba lalle ne kowane lokaci ’yan takarar ne da kan su kan fito su bayyana alqawuran ba, akwai sojojin su na baka da kan tallata su, su ambaci duk wani abu na alheri da za a kawo in an samu nasara amma in a ka hau ba mamaki sai ka ga burinsu a miqa mu su mukamai a ma’aikatu masu romon kasafin kuɗi su azurta kan su yayin da talakawa ke can su na ta hamma.

Abun lura a wannan sabuwar siyasar ko in ce a zaɓen Nijeriya na 2023 akwai wani sauyin loga da na gano inda masu zaɓe kan wuce kan ɗan takara su koma duba waɗanda ke kewaye da ɗan takarar. Misali ko da batun ɗan takarar jam’iyyar gwamnati Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki musulmi a matsayin mataimaki hakan ya jawo caccaka daga wasu mabiya addinin kirista a arewa; ya kai ga an shiga bayanan ai matar sa Kirista ce don haka shi ba mai nuna bambancin addini ba ne.

Shi kan sa ya fito ya yi bayanin hakan da nuna matarsa da ’ya’yan sa mabiya addinin Kirista ne. Shi kuma ɗan takarar PDP Atiku Abubakar an faɗaɗa da nuna ya auri wasu da ba ’yan ƙabilarsa ba daga wasu sassa na Nijeriya don haka ya nuna ba ya nuna ƙabilanci. Haka lamarin ya shafi ɗan takarar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso da a ke cewa ya na zagayawa don duba lamuran ’yan Arewa don haka wasu ajin jama’a ne masu tafiya ci rani kudu ke mara ma sa baya. Masu kare shi su ka nuna a’a ai ya ɗauki mataimaki ɗan kudu kuma fasto wani malamin majami’a.

Shi kuma ɗan takarar Leba Peter Obi na samun zargin ai magoya bayansa na mara baya ga ’yan awaren Biyafara masu kashe ’yan Arewa. Nan masu kariya su ka ce ba haka ba ne kuma wannan dalili ma ya sa ya shigo har Kaduna tsohuwar helkwatar arewa ya dau Dr. Datti Baba Ahmed a matsayin mataimakin takara.

Don haka a kan karanta ’yan takarar da duba abokansu, muƙarrabansu, mutanen gidajensu ba kawai abun da su ka ambata da bakinsu ba.

Yanzu kai tsaye za mu shiga batun Peter Obi wanda babban jami’i na biyu a kamfen ɗinsa wato daraktan kamfen ɗin gaba ɗaya Doyin Okupe ya yada ƙwallon mangoron aikin don kar hakan ya jawa tafiyar kamfen ɗinsu ƙarin kudaje.

Tun a watan Oktoba matasa magoya bayan Obi su ka ƙi amincewa da naɗa tsohon daraktan labaru na rundunar sojan Nijeriya Mnajo Janar John Enenche mai ritaya a matsayin memba na kamfen ɗin jam’iyyar.

Masu caccakar Enenche na cewa ya taka rawa lokacin ya na aiki na nuna sam sojoji ba su buɗe wuta kan masu zanga-zangar ENDSARS a Lekki a Legas ba. Matsa lambar matasan ya sa Enenche ya yi murabus daga muƙamin ya na mai bayyana cewa lokacin da ya yi bayanan ya na cikin kayan sarki ne don haka ya zama wajibi ya mutunta rantsuwar da ya yi ta kare muradun rundunar sojan Nijeriya.

Enenche daga jihar Binuwai wanda ba lalle ne ya fita daga harkar kamfen ɗin ba amma ya zama alatilas ya ajiye mukamin da a ka ba shi don matasan Obi ba su yarda da rawar da ya taka a lokacin zanga-zangar ba.

Ko a nan za a fahimci yadda muradun ’yan takarar ya ke kan lamuran da ke faruwa a ƙasa da hakan kansa da zarar wasu sun hango wani da ba su amince da shi ba sai su yi kuwa cewa a kawar da shi. Hakan ya ɗauki hankali ne da ganin tamkar mutane sun farka daga bin ɗan takara kaɗai, su kan duba muƙarrabai don su kan taka gagarumar rawa a gwamnati in an samu nasara.

Daraktan kamfen ɗin ɗan takarar jam’iyyar Leba Doyin Okupe ya yi murabus daga mukaminsa na daraktan kamfen ɗin jam’iyyar. Hakan na kunshe ne a wasiƙa da ya aikawa ɗan takarar Peter Obi ya na mai cewa ya yi ayyuka da dama da ba zai bari dalilansa na kashin kai su karkatar da kamfen ɗin ba.

Babbar kotun tarayyar Nijeriya a Abuja ta samu tsohon mai taimakawa shugaba Jonathan kan farafaganda Doyin Okupe da laifin zambar maƙudan kuɗi da ya karva daga ofishin tsohon mai ba da shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Okupe gaban kotu da caji 56 inda alƙalin kotun Ijeoma Ojukwu ta same shi da laifuka 26 da kuma umurnin ɗaurin shekara 2 kan kowane laifi.

Cajin ya nuna Okupe wanda a halin yanzu ya yi murabus a matsayin darakta na kamfen ɗin ɗan takarar jam’iyyar Leba Peter Obi, ya karɓi Naira miliyan goma-goma har kuɗi su ka kai Naira miliyan 240.

Alƙalin ta ce Okupe bai wahalar da kotu ba don ma ya nuna bai san kuɗin da ya karɓa laifi ba ne, amma rashin sanin doka ba ya zama uzurin da zai wanke wanda a ke tuhuma da aikata laifi a ƙarƙashin dokokin Nijeriya.

Duk da haka kotu ta ba wa Okupe zaɓin biyan tarar Naira dubu 500 ga kowane caji inda kuɗin su ka tashi Naira miliyan 13.

A ranar da a ka yanke hukuncin kotu ta ba da zuwa ƙarfe 4:30 na yamma matuƙar Okupe bai kawo kuɗin tarar ba a tura shi gidan yari ya fara zaman shekarun da a ka yanke ma sa.

Mai shari’a Ijeoma ta ƙara da cewa an samu wasu manyan ƙasa sun sa baki kan shari’ar ta Okupe hakanan matar Okupen ma ta roƙa a yi ma sa a yi ma sa sassauci. Abun da bai fito fili ba zuwa yanzu shi ne shin Okupe ya biya tarar ko ya na shirin shiga gidan yari.

In dai a nazari ne ko hasashe za a ce Okupe ya biya tara tun da har ga wasiqa ya turawa Peter Obi ta murabus ɗinsa daga kamfen haka kuma ai ba tsada ma a tarar don wanda a ka samu da laifin badaƙalar Naira miliyan 240 ya dawo da miliyan 13 ai tamkar tukuici ya bayar.

Kuma haƙiƙa masu son samun kuɗin bulus na gwamnati in za su samu irin wannan dama ta su sace miliyoyi amma in an roka kotu ta daura mu su ’yar tara irin wannan za su yi maraba da hakan da neman kuɗin “an zo a ci na banza” in ya so sai a bi kalmomin nan mai cewa GAFIYA TSIRA DA NA BAKIN KI.

Na kalli zantawar da gidan talabijin ɗin Tambarin Hausa ya yi da shugaba Buhari inda mai tambaya tsohon ɗan jarida Halilu Ahmed Getso ke neman a amsa ma sa tambayar gaskiyar yaƙi da cin hanci na gwamnatin nan inda da ya ga bai samu amsar da ya ke buƙata ba sai ya faɗaɗa da cewa har ma an yafewa wasu.

Shugaba Buhari dai bai ɗauki batun yafewar ba amma ya ce ai ya sauya manyan alƙali biyu kuma ai in ya yi gyara daga manyan to nagari a cikin su za su gyara ƙanana. Ni dai tunani na ya je ga batun yafewa tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame ne a ke nufi a nan.

Shugaba Buhari da Kalmar yaƙi da cin hanci ta zama kan gaba a alƙawuran sa ya ce matuƙar a ka kawo hujjar mutum ya zarme to gwamnatin za ta hukunta shi. Duk mun san dalilan da su ka saka har tsohon babban alƙali Walter Nkanu Onneghen ya rasa muƙamin sa to ba mu san dalilin da ya sa tsohon babban alƙali Tanko Muhammad ya yi murabus ba fiye da cewa ba shi da ƙoshin lafiya.

Wasu labarun na gwamnati fa sai wanda ya san gwamnati ko a ke damawa da shi kaɗai zai sani. Kuma in abu bai shafe ka ba bar shi a inda ka gan shi matuƙar ba irin wanna n sharhi ya kawo batun ko ɗan jarida ne na rubuta rahoto ba.

Kammalawa;

Ko waye zai kai gaci daga irin jama’ar da ke zagaye da shi a cikin ’yan takarar shugabancin nan? lokaci ne zai nuna. Mu dai na mu shi ne Allah ya zabawa Nijeriya mafi alheri su kuma ’yan takara sai mu ce Allah maɗaukakin Sarki ya ba wa mai rabo sa’a.