2023: Mutanen kirki kaɗai za ku zaɓa, Sarkin Musulmi ga ‘yan Nijeriya

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zaɓi mutane nagari masu kishin ƙasa a matsayin shugabanni a zaɓe mai zuwa.

Ya bayyana haka ne a wajen bikin Saukar Karatun Alƙur’ani na mahadata 825 da Makarantar Hizburrahim gudanar cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa, Jihar Katsina.

Basaraken ya ce, zaɓen 2023 ya ƙarto don haka akwai buƙatar jama’a su fito don su zaɓi nagartattun shugabanni waɗanda za su jagoranci ƙasa wajen ficewa daga halin da tale ciki.

A cewarsa, “Yau ƙasarmu na neman wanda zai ceto ta daga mawuyacin halin da take ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki da tsaro, a kan haka ake kira ga al’umma musamman masu zaɓe da su zabi mutane nagartattu.”

Daga nan, ya yaba wa malaman wannam makaranta dangane da ƙoƙarin da suke yi wajen karantar da matasa ilimin Alƙur’ani.

Sarkin ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ji tsaron Allah su taimaka wa cigaban addini da makarantun addini don samun al’uma tagari .

Ya bayyana alwashin na taimaka wa makarantar wajen magance matsalolinta da samar mata cigaba mai ɗorewar .

Anasa jawabin Daraktan Makarantar, Khalifa Aliyu Saidu Alti Funtua, ya bayyana godiyarsa ga Sarkin Musulmi da ya zamo uban taro na bikin.

Kana ya yi kira ga shugabanni da su taimaka wajen samar da tsaro domin samun dawamammen zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.