Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano
Ƙungiyar Tsofaffin Kansilolin Ƙananan Hukumomin Jihar Kano 44 na shekara ta 2018 zuwa 2021 ta yi kira ga gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Mai girma gwamna Dk. Abdullahi Umar ganduje ofr Kadimul Islam, gwamnati Mai adalci da ta taimaka ta cika alqawarinta na biyan tsoffin kansilolin haƙƙinsu da suka ƙarƙare mulki a shekara ta 2021.
Mai magana da yawu na ƙungiyar, Tsohon Kansila daga mazaɓar unguwa uku Ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Garzali abdull-rahman Dogo, shine ya yi wannan koke ga gwamnatin, a madadin sauran kansilolin cikin hirarsa da manema labarai, ciki kuwa har da jaridar Blueprint Manhaja, a ranar asabar ɗin makon da ya gabata.
Hon. Garzali dogo, wadda ya yi furicin cikin damuwa, ya ya ce ƙungiyar kansilolin ta bi matakai iri daban-daban na ganin gwamnatin ta biya su haƙƙinsu wato masamman a ta hanyar zama da masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasar yau da kullum na jihar, tare da shiga wato kafafen watsa labarai, don ganin an biyasu haƙƙinsu, amma har kawo yanzu babu wani albishir daga gwamnatin.
A cewarsa la’akari da halin da ƙungiyar ta su ke ciki a halin yanzu, kamata ya yi gwamnatin tayi dube na tsanaki, wajen ganin ta share masu hawaye masamman a dai-dai wannan gaɓa ta tunkarar zaɓen shekara ta 2023.
Daga bisani Hon. Garzali dogo, ya yi addu’ar fatan alheri ga kasa dama jihar ta Kano, na ƙara samun wanzajjen zaman lafiya.
