Buhari ya taya Ganduje murnar cika shekara 73 da haihuwa

Daga WAKILINMU

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje murnar cika shekara 73 da haihuwa.

Buhari ya yi hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ta bakin mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ranar Asabar a Abuja.

Ya kuma yaba wa Gwamnan bisa salon shugabancinsa da kuma ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi a Kano, tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Daga nan, ya yi kira ga Gandujen da ya ci gaba da bai wa walwalar talakawan jihar muhimmanci da bunƙasa jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *