Burina na yi ficce a harkar fim, don ba abinda zuciyata ke muradi sama da shi – Fatima Musa

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Fatima Musa da aka fi sani da Salima sanadiyyar fitowar ta a cikin fim ɗin nan mai dogon zango mai suna ‘Sirrin Ɓoye’ Fatima wacce ta samu sha’awar finafinan Kannywood tun tana ƙarama. A tattaunawar ta da wakilin Manhaja a Kano, za ku ji cikakken tarihinta da kuma irin ƙalubalen da ta fuskanta har zuwa wannan lokacin. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Da wa muke tare?

FATIMA MUSA: Ni sunana Fatima Musa, an haife ni a Ƙaramar Hukumar Damasak ta Jihar Borno, na yi Primary da Secondary duk a can, sannan na yi makarantar gaba da sakandare mai suna Ramat Polytechnic inda na karanci ‘Agric and Environmental Engineering’.

Ta yaya ki ka samu kanki a masana’atar Kannywood?

To, ni dai gaskiya tun Ina yarinya na ke sha’awar yin fim, to da na shigo Kano, sai na fara yi kuma tun daga Maiduguri fim ne ya Kano.

A wacce shekara ki ka fara fim?

Na fara fim shekaru uku da suka wuce, domin a shekarar da zo Kano na fara.

Ko da sanin iyayenki ki ka shigo Kano?

Eh da sanin iyayena na shigo Kannywood, duk da yake iyayena sun rasu, amma da sanin yayyena da ‘yan’uwa dukka.

A lokacin da ki ka shigo masana’antar ta Kannywood ba ki ci karo da ‘kan tawaye’ ba?

Gaskiya ni kam ban faɗa wannan komar ba, ma’ana ba a yi min ‘kan tawaye’ ba, domin na samu ubangida na gari, saboda lokacin da na shigo Kannywood na sayi form na shiga ne, sannan na shiga. Don haka ni na samu ubangida na gari, saboda haka ni ba ai min ‘kan tawaye’ ba.

Da wane fim ki ka fara?

Na fara ne da wani ƙaramin fim, wato ‘short Film’ a turance, wanda Ina gida ubangidana ya kira ni aka fara ɗora min ‘Camera’.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ki ka yi?

Ya zuwa yanzu na yi finafinai aƙalla guda takwas, kaɗan daga ciki su ne: ‘Sirrin Ɓoye’, ‘Macen Sirri’, ‘Neman Duniya’, ‘Halacci’ da sauransu.

Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu, waɗanne irin nasarori ki ka samu?

To, a wannan ɓangare kam ba abinda zan ce sai alhamdu lillah. Na samu nasarori da yawa, duk da yake kafin na shiga na nemi aiki ban samu ba, to amma yanzu na samu aikin yi, domin kuɗin kashewa da kuɗin kati da kuma ɗan kuɗin taimaka wa ‘yan’uwana, alhamdu lillahi, gaskiya Ina samu, ba abin zan ce wa Allah sai godiya don gaskiya mun gode wa Allah da ni’imar da ya yi mana.

Wane irin ƙalubale za ki iya cewa kin samu shigowar ki Kannywood?

Eh gaskiya na haɗu da ƙalubale, da yake lokacin da fara fim iyayena duk sun rasu, Ina ƙarƙashin kulawar yayyena ne, to a lokacin da aka fara ganina a tashar Arewa24, ɗauko fim ɗin aka yi, aka sanya a tsakar gida, ake cewa ga abin da na koma yi. Lokacin da na koma gida suka sanya ni a gaba suna ta yi min faɗa, to a hankali a hankali na wayar masu da kai, na nuna masu cewa fim sana’a ce, to fa sannan ne suka fahimce ni. Don haka shigowa harkar fim tsundum da sanin iyayena.

Wane ne maigidanki a Kannywood?

Maigidana shi ne, Maje EL-Hajjij Hotoro, mai kamfanin Sirrinsu Media, domin shi ya fara saka ni a fim.

Menene burinki da ki ke son cimma a masana’atar Kannywood?

Burina a Kannywood shi ne, na zama ‘Super Star’, ya kasance na zama fitacciya, don ni a gaskiya ba abinda zuciyata ke muradin yi sama ga ‘acting’.

Menene kiran ki ga abokan aikinki da kuma masoyanki?

Kira na ga abokan aikina shi ne, mu haɗa kai, mu jure, mu yi haquri, sannan mu jure, in Allah ya yarda abinda muke nema Allah zai tabbatar mana, kuma duk mai haquri ba ya faɗuwa. Su kuma masoyanmu, muna gode masu kan soyayyar da suke nuna wa gare mu, kuma su ci gaba da ba mu shawarwari kan inda suka ga munyi kuskure.

Muna godiya.

Ni ma na gode sosai.