Babu sana’ar da ke kawo min kuɗi kamar ta sabulai – Hauwa Dashiru

Spread the love

“Ban samu karɓuwa ba sai lokacin da gwamnati ta kafa dokar hana yawo lokacin Buhari “

Daga UMAR AKILU MAJERI 

Hajiya Hauwa Dashiru Muhd wata Hajiya ce a cikin mata a Jihar Jigawa da ta yi suna wajan gyaran jiki musamman yadda ake wa mata masu shirin amarcewa gyaran fata.

Hajiya Hauwa ta shahara a wannan daɓe na yi wa amare dilka, gyaran gashi, turaren mata da tiraren jiki da haɗa humra da nufin kyautata dangantaka tsakanin amarya da ango a gidajen aure.

Wakilinmu na Jihar Jigawa ya samu tattaunawa da Hajiya Hauwa Dashiru akan yadda takeyiwa amare gyaran jiki da gyaran gashi, ta kuma gaya wa masu karatu lokacin da ta fara yin sana’ar,ar. Idan kun shirya, a sha karatu lafiya;

MANHAJA: Hajiya masu karatu za su so sanin tarihinki a taƙaice.

HAJIYA HAUWA: Sunana Hajiya Hauwa Dashiru Muhd. Ina yin aikin dilka da gyaran jikin amarya. Na fara yin wannan sana’a tun Ina budurwa, kuma na kafa kanfanina mai suna 3MA, na yii amfani da sunayen yarana wadda nake yin kasuwancina ta yanar gizo wato online trading.

Ina yin humra da tiraren gyaran jiki da tiraren mata da sabulun wankin kai da na wanke mota da banɗaki.

Amma a duk sana’ata babu wadda ta fi kawo min kuɗi kamar sana’ar sabulai, in ka ɗauke sana’ar gyaran jiki da nake wa amare.

 Kenan bayan gyaran jiki kina wasu sana’oin?

Ina yin yajin tafarnuwa da haɗa kayan ƙamshi wadda nake dakawa ake sara awajena, su kuma suke sanyashi a pakeji su aika da shi wasu wuraren domin sayarwa yayinda wasu lokutan ake aikawa da su wasu jihohin.

Yaushe ne kika fara yi wa mata gyaran jiki da dilka?

Na fara sana’ar gyaran jiki da dilka tun Ina budurwa, amma ban samu karɓuwa ba sai lokacin da gwamnati ta kafa dokar hana yawo lokacin Buhari ‘lock down’ a wannan lokacin ne na samu ɗaukaka saboda an hana yawo a wannan lokacin ne na samu damar tallata abinda nake yi ta hanyar yanar gizo, shine Allah ya yi min nasibi mutane daga Kano, Bauchi da kuma nan gida Jihar Jigawa.

Yanzu da Kano da Jigawa na shahara a fuskar gyaran jiki, domin har gida sna zuwa ana ɗaukata domin yiwa amarya gyaran fata na mayar da jikinta tamkar an yi mata gugar injin.

Da nawa kika fara gyaran jiki?

Na fara gyaran jiki tun Ina karɓar Naira dubu uku a matsayin kuɗin aiki a lokacin komai yana da sauƙi.

Yanzu a nawa kike aikin gyaran jikin amarya da yake yanzu komai yana tsada?

Yanzu idan kwana ɗaya ne Naira 20,000, amma idan kwana uku be kamar yadda nake yi, Naira N50,000. Amma wannan farashin buduwa ne, amma su zawarawa Ina yi masu gyaran jiki ne akan Naira dubu ashirin zuwa dubu talatin domin nasu ba kamar na budurwa ba ne saboda su ba a yi masu dilka.

Ko kina yiwa matan aure gyaran jiki?

Ina yi wa matan aure gyaran jiki domin gyaran jikin da halawa yana sa mata laushin fata da sheƙin fata hakan yana ƙara danƙon zamantakewa tsakanin ma’aurata.

Sau da yawa mazaje ne suke kawo matansu, kuma su biya, amma su nasu bai kai na amarya tsadaba, saidai idan matar ba a taɓa yi mata ba ita ma farashinta daban ne domin za a yi mata aiki sosai, kuma za a wahala. 

Ko ana ɗaukar ki ki je gida ki yi wa mata gyaran fata ko dilkar da halawa?

Gaskiya Ina zuwa, amma zai fi tsada tunda ɗaukata ake yi ko amarya ko bazawarar da zata yi aure ko matar gida farashinta daban yake.

Su ne za su ban kuɗin mota da kuɗin abinci da kuɗin barin ‘office’, saboda nabar gida wannan wani sir charges ne da ake ɗora wa akan ainahin kuɗin aikin da ake biya na. 

Ko matan aure suna zuwa gunki sosai?

Sau da yawa matan suna zuwa gyaran jiki, amma mafiya yawan su sun fi dogaro da mayukan shafe-shafe.

A ina ne kika koyi sana’ar gyaran jikin amarya?

Na koyi wannan sana’a a wajan wata mata aminiyata ‘yar Chadi. Kuma har gobe ina yin alfahari da ita, domin ta saka ni a hanyar arziki wanda nake amfanar da zuriyata suke cin moriyar abinda ta gwada min. 

A inakike sayan kayan aikinki

Ina sayan kayan aikina daga Chadi saboda kayansu ya fi namu na Nlnan gida inganci. Kuma na su yana da matuƙar kyau sosai ban taɓa yin amfani da kayansu na sami wata mishkila ba shi ya sa nake jin daɗin amfani da kayansu. Kuma nake yin amfani da su.

Zuwa yanzu ko kin san yawan waɗanda suka koyi sana’ar gyaran amarya a wurinki?

Na gwada wa mata da ‘yan mata wannan sana’a a Jihar Kano da Jigawa masu yawa wasu ma sun fini ƙwarewa, amma da yake na shahara jama’a da yawa inba nice na yi masu ba ba sa amincewa da wata ta yi wa ‘yarsu gyaran jiki musamman budurwa saboda yadda nake yin aikina ya sha bamban da nakowa.

Ko kina yiwa maza gyaran jiki kamar yadda kike yiwa mata?

Ba na yiwa maza gyaran jiki, amma Ina haɗa kayan in ba su da bayanan yadda za su yi da kansu suje suyi ko ‘yan uwansu maza su yi masu ko matansu a gida suyi masu. Amma ni ba na yi wa maza gyaran jiki.

Ni dai ina yiwa mata kuma Ina haɗa maganin gyaran fuska da nake sayarwa kowa daga ‘yan mata samari da zawarawa da matan aure kuma akan farashi mai sauƙi.

Bayan gyaran jiki wacce sana’a ce ta fi kawo maki kuɗi?

Sana’ar haɗa sabulun wanki da wanke-wanke da gyaran banɗali da sabulun wanke mota ita ma sana’a ce da take kawomin kuɗi domin kafin na shahara akan gyaran jikin amarya da ita na dogara sana’a ce da take kawo kuɗi, amma da yake an yi yawa a kanta ta sai kasuwar ta cushe ya zama babu kasuwa.

ƙasashe nawa kika je a rayuwarki?

Ni ban taɓa zuwa wata ƙasa ba duk kasuwancina anan gida nake yi, nan Nijeriya, amma shigata ƙungiyar Nasal shi ne ya sa aka sanni a harkar gyaran jikin amarya.

Ko menene shawararki ga mata ‘yan kasuwa?

Shawarata ga mata, su dogara da kansu su zama masu yin sana’ar hannu.

Yanzu wanne albishir zaki yiwa masu so da siyan kayan da kike yi?

Ina yiwa jama’a albishir zan kawo masu lemukan sha na garganiya masu inganta lafiya waɗanda zan yi su da kayanmu na garganiya, kamar busassiyar gwanda da zobo da tsamiya da kuka da sauransu. 

Na gode. 

Ni ma na gode.

By ukarofi