Sarkin Musulmi ya buƙaci ICPC ta rungumi dabarun zamanin ƙwato kadarori

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da ta inganta tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa ƙoƙarin ƙwato kadarori da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Abubakar ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamishinan yaƙi da cin hanci da rashawa na ICPC mai kula da Sakkwato da Kebbi, Shintema Binga, ranar Litinin a Sakkwato.

Ya kuma buƙaci hukumar ta ICPC da ta tabbatar da cikakken tsarin tafiyar da yaƙi da cin hanci da rashawa, yana mai jaddada cewa akwai buƙatar a tallafa wa fafutukarta a dukkan matakai.

Ya kuma tabbatar wa hukumar samun cikakken goyon baya daga sarakunan gargajiya wajen rage cin hanci da rashawa ta kowane fanni, ya kuma ja kunnen hukumar kan ayyukan da ke kawo illa ga gwagwarmayar ta.

“Dole ne hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su yi nasara, a shirye muke mu tallafa musu a kowane mataki, Majalisar Sarkin Musulmi ta sake buga littattafan da Sheikh Usman Danfodio da almajiransa suka rubuta kan cin hanci da rashawa.

“Irin waɗannan litattafai tabbas za su bayar da hujjar gwagwarmayar yaƙi da ayyukan cin hanci da rashawa da suka taso a cikin al’ummarmu,” inji shi.

Sultan ya umarci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su kasance masu gaskiya a cikin harkokinsu, ya ƙara da cewa sarakunan gargajiya a shirye suke su ba su goyon baya da kuma tsayawa a ko ina.

Yayin da ya ke jawabi tun da farko, kwamishinan ICPC ya ce yaƙin da hukumar ke yi da cin hanci da rashawa shi ne jigon gudanar da shugabanci nagari da kuma ci gaban ƙasa

Binga ya yaba da goyon bayan Sultan ga yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya kuma yaba wa Sarkin Musulmin bisa jagorancin sarakunan gargajiya a lokuta daban-daban a karon farko na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ƙara da cewa, hukumar na wayar da kan ‘yan Nijeriya kan illolin cin hanci da rashawa.

By ukarofi