Maryam Abacha ta magantu akan zargin mijinta da hannu a badaƙalar kuɗaɗe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matar marigayi tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, wato Inna Maryam Abacha, ta musanta zargin batun cewa mijina ya yi almundahanar biliyoyin daloli a lokacin da ya ke shugaban ƙasa.

A hira da ita ta gidan TVC a ranar Lahadi, ta bayyana zargin da aka yi wa mijin nata a matsayin rashin adalci da kuma ƙoƙarin ruɗar da al’umma.

Ta yi ƙalubalen cewa, babu wata hujja ta kai-tsaye da ke tabbatar da Abacha ya yi almubazzaranci da dukiyar ƙasa, tana mai ƙalubalantar bututuwan da ke cewa an sace biliyoyi da kai su ƙasashen waje a zamaninsa.

Ta kuma ce, soke zaɓen da aka yi gabannin hawan Abacha mulki ba shi ya aikata ba, wanda idan dai shi ne, to hakan ya nuna cewa ya fi iko akan shugaban ƙasa na wancan lokacin, tana mai nanata cewa lallai mijinta bai aikata haka ba.

Maryam Abacha ta kuma yi kira da haɗin kai da mutunta juna a tsakanin al’ummar Nijeriya, inda ta koka da tasirin son kai na ƙabilanci da addini a yayin gudanar da tattauna muhimman al’amuran ƙasa.

Haka kuma, ta nuna damuwa game da yadda al’amarin rashin tsaro ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar duk da ƙarfin soja ta take da shi, tana mai cewa hakan bai sa ta kawo ƙarshen ƙungiyoyin ƴan ta’adda ba.

Ta yi nuni da buƙatar samar da alaƙa mai ƙarfi a tsakanin gwamnatin mulkin farar hula da ta sojoji wajen kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro.

By Babaji