Gwamnan Gombe ya yi tir da kisan Amadi Kasiran daga ɓata-gari da umarnin a farauto su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya yi alla-wadai d kisan Ahmed Aliyu mai shekaru 45, wanda aka sani da Amadi Kasiran da wasu ƴan daba suka farmaka a yankin Hammadu Kafi dake cikin garin Gombe.

Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Yuni, inda aka daɓa wa mamacin wuƙa, lamarin da ya sa aka garzaya da shi babban asibitin Specialist inda aka tabbatar da mutuwarsa, kamar yadda muryoyi daga hukumomin tsaro suka bayyana.

A lokacin da ya ke magana game da al’amarin, Gwamna ya koka tare da bayyana alhininsa, yana mai bayyana kisan a matsayin abinda aka yi babu lissafi kuma wanda ba za a amince da shi ba.

Ya ci alwashin cewa, gwamnatinsa ba za ta bari ayyukan dabanci ya sake ɓarkewa a jihar ba.

Gwamna Inuwa ya ce, kisan barazana ce ga zaman lafiyar al’umma a jihar don haka za su ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu a ciki.

Kazalika, ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta farauto masu laifin domin su fuskanci hukuncin doka tare da sauran masu aiki irin nasu.

By Babaji