Mataimaki ga Tinubu ya yi murabus, ya jinjina wa Ajuri Ngelale

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne Babban Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan Harkokin Al’umma, Aliyu Audu ya ajiye aikinsa.

A wani saƙon shafi ɗaya da ya fitar a ranar 8 ga watan Yuni, Audu ya bayyan cewa ya yi murabus, wanda hakan zai fara aiki ne a nan take.

Sannan ya yi wa Shugaban ƙasar godiya bisa ba shi damar yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashinsa.

Ya kuma yaba wa tsohon kakakin Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, wanda shi ne ya bada shawara aka ba shi muƙamin a watan Agustan 2023.

Kazalika, ya yi addu’ar fatan alkhairi da cigaba da samun nasara ga gwamnatin Tinubu domin amfanin al’ummar Nijeriya.

By Babaji