12
Mar
Fatima Yusuf Muhammad ta kasance mace mara kasala wajen fafutikar neman ilimi, sana’ar dogaro da kai da kuma faɗakar da al’umma da nishaɗantar da su ta hanyar rubuce-rubucen littattafan hikaya. A wannan makon Manhaja ta yi wa masu karatu kiciɓis da ita don jin yadda ta ke jifar tsuntsaye uku da dutse ɗaya, ma’ana ga neman ilimi da ta sa gaba, sana’a da kuma rubutu, ga kuma ɗawainiyar iyali. Kai, wani aiki dai sai mai shi. Ga yadda tattaunar ta kasance: Masu karatu zasu so jin tarihin ki.Ni dai suna na Fatima Yusuf Muhammad. An haife ni a garin Kaugama…
